Dalilin da ya sa Buhari bai ce komai ba kan zargin kisan mutane a Lekki

0

Kakakin fadar shugaban kasa Garba Shehu ya ce har yanzu ba a gama bin diddigin ainihin abin da ya faru a Lekki tukunna a wanna dare da aka ce sojoji sun yi kisan masu zanga-zanga ba.

Ya ce Buhari ba zai yi hukunci da jita-jita ba, duka jami’an tsaro na gudanar da bincike akai sannan kuma ita kanta jihar Legas ta kafa kwamiti domin yin bincike akai.

Da zarar an tabbatar da abinda ya faru, gwamnati zata bayyana matsayinta akai.

Bayan haka shugaba Buhari ya yaba wa jami’an ƴan sanda da suka cafke sama da mutum 200 da aka kama suna barnata kadarorin gwamnati da sunan zanga-zanga #EndSARS.

Wasu da dama na sukar shugaba Buhari kannkin cewa komai da bai yi ba game da zargin kisan masu Zanga-Zanga #EndSARS da sojoji suka yi da bai yi ba.

Sai dai kuma har yanzu masu korafin basu iya kawo koda mutum daya ba da aka ce an kashe a wannan wuri.

Hatta masu korafin cewa suna wurin sun kasa nuna mutum daya da za su ce an kashe shi a wannan wuri amma kuma sun ruruta abin kamar akwai hujjoji da suke da shi.

A dalilin haka ne shugaba Buhari ya ce bazai komai akai ba, sai kwararru sun bi ba’asi, sun yi binciken kwa-kwaf and tabbatar da harbi, da kuma wadanda aka ce an kashe su a wurin, gawar su ko kuma ƴan uwan su.

Share.

game da Author