Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Zamfara ta bada sanarwar cewa wasu gungun ƴan bindiga sun yi garkuwa da Hakimin Lingyado da ke cikin Karamar Hukumar Maru.
Kakakin ƴan Sanda na jihar, Mohammed Shehu ya ce ‘yan bindiga sun yi tattaki har gida su ka tafi da shi da karfin tsiya, a ranar Lahadi, wajen karfe 8 na safe.
Ya ce sun kuma yi gaba da wasu mutum hudu tare da Hakimin.
“Rundunar Hada-ka ta ƴan sanda da sojoji da ke kusa da garin ta kai daukin gaggawa bayan da aka sanar da ita cewa ‘yan bindigar sun isa garin.
“Ba don gaggawar da jami’an tsaron su ka yi ba, da wadanda masu garkuwa za su tafi da su, su na da yawa sosai.”
Haka Mohammed Shehu ya sanar a sanarwar manema labarai da ya fitar, kuma bai bayyana sunan Hakimin da sauran mutum hudu da aka gudu da su ba.
Amma dai jama’ar gari sun tabbatar da sunan hakimin Dalha Danjago.
Kakakin ƴan sanda ya yi kira ga jama’a su kai rahoton duk wani motsi da ba su amince da shi ba.
Ya ce ƴan sanda da sojoji sun bazama cikin dazuka domin ceto hakimin da sauran mutum hudu da aka yi garkuwa da su tare.
Wannan al’amari ya zo mako daya bayan da ‘yan bindiga su ka kashe mutum 22 a kauye ɗaya a rana daya, kuma a lokaci daya a Zamfara.
Discussion about this post