OHANEZE TA CI KWALAR BURATAI: “Ba ka isa ka kakaba Dokar-ta-baci a Kudu maso Gabas ba”

0

Kungiyar Kare Muradin Kabilar Igbo Zalla, Ohaneze Ndigbo, ta shaida wa Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Tukur Buratai cewa ba shi da karfin ikon da zai kakaba wa yankin Kudu maso Gabas dokar-ta-baci.

Kungiyar na maida wannan martani ne bayan an ruwaito Laftanar Janar Buratai na barazanar kakaba dokar-ta-baci a yankin Kudu maso Gabas.

Cikin watan Agusta an kashe jami’an SSS biyu a Enugu a lokacin wata arangama tsakanin jami’an tsaro da ‘yan Kungiyar Rajin Kafa Jamhuriyar Biafra (IPOB).

An kuma kashe wasu mambobin IPOB din a wurin arangamar, tare da ji wa da dama raunuka, sannan aka kama wasu masu yawa.

Dama kuma kafin wannan arangamar, akwai rahotannin da ba a tabbatar ba da ke nuna cewa an rika kai wa jami’an tsaro musamman sojoji hari a Enugu.

Rahoto kuma ya tabbatar da cewa Buratai ya harzuka da wannan rahotannin hare-haren da aka ce an kai wa sojoji, har ya yi barazanar kakaba dokar-ta-baci a Kudu maso Gabas, idan aka ci gaba da kai wa sojoji hare-hare.

PREMIUM TIMES ta ba tabbatar da ko Buratai ya yi wancan furuci na kakaba dokar-ta-baci ba.

Sai dai a cikin takardar da Ohaneze ta fitar mai dauke da sa hannun Sakataren Yada Labarai na kungiyar, Uche Achi-Okpagha, ya ce har yau Buratai bai fito ya karyata ikirarin da aka ce ya yi na barazanar kakaba dokar-ta-baci din ba.

Kungiyar ta ce furucin na Buratai kamar “wani tsokanar fada ne, da har zai yi barazanar kakaba dokar-ta-baci a yankin da ake zaune lafiya, amma bai yi hakan a Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas ba, yankunan da ake fama da gumurzun yaki da Boko Haram, mahara, ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane, masu kashe sojoji da fararen hula.”

Kungiyar kuma ta nuna mamakin inda Buratai ya samu karfin ikon kakaba dokar-ta-baci, wadda sai shugaban kasa ne kadai doka ta bai wa wannan karfin iko.

Share.

game da Author