Kungiyar Kwadago ta baiwa gwamnati tarayya kwanaki 14 ta janye karin kudin man fetur da wutan Lantarki

0

Kungiyar Kwadago ta Kasa ta baiwa gwamnatin tarayya, kwanaki 14 ta janye karin kudin man fetur da na wutan lantarki ko kuma ta fara yajin aikin gama gari a kasar.

Shugaban Kungiyar Kwdaga Ta Kasa, Ayuba Wabba ya shaida cewa kungiyar ta amince ta fara yajin aiki nan da kwanaki 14 idan gwamnatin tarayya bata janye karin kudin man fetur da tayi da na wutan lantarki ba.

” Maimakon ace tallafawa mutane ake yi da kayan abinci a dalilin matsin da aka fada saboda annobar Korona da ya saka mutane da dama cikin matsaloli, gwamnati ta rika tallafa musu sai kawai ta kara kudin mai fetur da wutan lantarki sannan a lokaci daya. Yaya ake so talaka yayi a kasar nan.

” A dalilin haka bayan tattaunawa da muka yi a tsakanin mu da sauran kungiyoyi da ke karkashin kungiyar kwadago mun tsayar cewa muddun gwamnati bata janye wadannan kari da ta yi ba nan da makonni biyu masu zuwa zamu shiga yajin aikin da za a garkame kasar gaba daya babu wani sashe da zai yi aiki.

Idan ba a manta gwamnati ta kara kudin man fetur daga naira 138 duk lita zuwa naira 161.68. Wannan kari ya sa an samu hauhawan farashin abinci da na masarufi. Komai ya yi tsada.

” Ace wai mutum ya siya wuta na naira 30,000 amma bai iya kaishi mako biyu ba a kasar nan. Ba zai yi ba haka za a cigaba da zama a zuba wa gwamnati ido sai yadda ta yi da mutanen kasa da talakawa. Ko ta janye ko mu fara yajin aiki na duk kasa.

Share.

game da Author