Yadda Femi Fani-Kayode ya rabu da matar da ya ke ji da ita, ta yi gaba da ‘ya’yan su hudu

0

An tabbatar da rabuwar aure tsakanin Femi Fani-Kayode da matar sa wadda ya ke ji da ita, ‘yar kabilar Igbo, mai suna Precious Chikwendu.

Ma’auratan dai sun kulla aure cikin 2014, kuma su na da ‘ya’ya hudu, na farko da kuma ‘yan-uku.

Majiya daga bangaren matar ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa auren ya yi mutuwar da ba zai sake kulluwa ba, saboda dalilai na batun lafiya, wanda tun da aka yi auren Precious ta yi ta maleji, har dai abin ya kai makurar kasa daurewa.

Majiyar ta ce batun rashin lafiyar ya rika haifar masu gagarimar matsalar da a karshe ta shiga wani mawuyacin hali.

Daga cikin dalilan mutuwar auren, ciki har da wadanda ba su buguwa a jarida, akwai matsalar yawan fitar da matar ke yi, ba tare da iznin Fani-Kayode ba.

Majiyar cikin iyali ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa matar, wadda ta taba wakiltar Najeriya a Zaben Sarauniyar Kyau ta Duniya a Majalisar Dinkin Duniya, cikin 2014, kafin auren su, ta rika fita ba tare da izni ba.

Wannan matsala ta haifar da rashin jituwar da a karshe ya kasa daurewa, su ka rabu.

Wata majiyar kuma cewa ta yi Precious ta bar gidan Fani-Kayode, saboda dukan da ya ke yawan lakada mata.

Amma wani dan uwan ta mai suna Okey Onyemachi, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa lallai sun rabu, “amma zargin ta na yawan fita da kuma ji-ta-ji-tar cewa wai ‘ya’yan guda hudu ba na Femi Fani-Kayode ba ne, na wani kato ne can daban, wannan duk karya ce.

“Ban taba sanin ya lakada mata duka ba, saboda bai doke ta din ba. Amma tabbas a yanzu sun rabu, ba ta gidan sa tsawon watanni da su ka wuce.

Precious dai ta taba fitowa a finafinai, kuma ‘yar kwalisa ce, sannan kuma Sarauniyar Kyau. An haife ta cikin 1989.

Kokarin jin ta bakin ta bai yiwu ba.

Share.

game da Author