Atiku da Ribadu za su zama sirikai duk da bambamcin ra’ayin siyasa dake tsakanin su

0

Diyar tsohon shugaban Hukumar EFCC Nuhu Ribadu da Dan tsohon Mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar za su zawwaje ranar Asabar mai zuwa.

A siyasance Atiku da Ribadu basu ga maciji a tsakanin su da hakan yasa ko jam’iyya daya basu iya zama ciki tare.

Duk lokacin da Atiku ya shiga wata jam’iyya tub daga 2011, Ribadu zai fice daga wannan jam’iyya ya koma wata.

A 2015 da Atiku marawa Jibirilla Bindow na jam’iyyar APC ne baya a zaben wanda Nuhu Ribadu na PDP a wancan lokaci ya fafata da shi, sai dai bai yi nasara ba.

Bayan Atiku ya koma PDP daga APC, Ribadu ya canja sheka zuwa jam’iyyar APC daga PDP wanda har yanzu yana cikin wannan jam’iyya.

Ko da yake iyayen Ango da Amarya ba su ce komai akai ba sai dai makusantan su sun shaida cewa bambamcin ra’ayi na siyasa bai hana ƴaƴan ci gaba da soyayya da juna ba.

Za a daura auren Aliyu Abubakar da Fatima Ribadu ranar Asabar.

Share.

game da Author