SABON LALE: El-Rufai ya ce a sake zaben sabon sarki, gwamnati bata amince da na baya ba – Sakataren gwamnatin Kaduna

0

Gwamnatin jihar Kaduna karkashin gwamna Nasir El-Rufai ta aikawa masu zaben sarki a masarautar Zazzau cewa su koma su sake zabo sabon sarki, cewa gwamnati bata amince da na farko ba.

Sakataren gwamnatin jihar Balarabe Lawan ya bayyana cewa gwamnati ba zata yi amfani da wannan sunaye ba gani saida aka yi wa duniya shelar abinda takardar ta kunsa kafin aka mika wa gwamnatin jihar.

Sannan da gangar aka yakice gidajen sarauta biyu wanda suma suna da damar a fafata da su wajen neman wannan kujera amma aka wancakalar da su saboda wasu shafaffu da mai.

Bunun Zazzau ya zargi masu zaben sabon sarkin da yin kumbiya-kumbiya wajen kin amsar takarada sa na neman kujerar sarautar Zazzau din. Da ya kawo wasikar sa sau suka ce masa yayi hakuri an rufe kofar karbar.

Haka kuma shima Sarkin Dajin Zazzau, wanda shima ya gaji sarautar, ya ce an ki a karbi tarakardar sa.

Bayan haka an gano cewa wasu shafaffu da daga cikin ƴan takaran an rattaba sunayen su tun kafin ma a karbi takardun su sabo da isa.

Saboda haka, masu zaben sarkin yanzu haka an sake aika musu da sunayen mutum 13 da suke neman sarautar Zazzau din su tantance su sannan su mika wa gwamnati domin bayyana sabon sarki.

Share.

game da Author