Ban ce Najeriya ta kusa rugujewa kowa ya kama gabansa ba – Boss Mustapha

0

Sakataren gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya karyata rahotanni dake yawo a kafafen yada Labarai cewa wai shi da mataimakin shugaban kasa sun ce Najeriya na gab da rugujewa kowa ya kama gabansa idan ba a yi wani abu akan irin matsalolin da suka dabaibaye kasar ba.

Mustapha ya ce ba ayi wa kalaman sa fassara masu kyau ba.

Ya ce ba a yi wa kalaman sa fassara mai kyau ba wanda yayi a coci wajen addu’ar cikar Najeriya shakaru 60 da samun ƴancin kai da kuma dorewarta kasa daya dunkulalliya.

” Ban ce haka, an yi wa kalamai na munanan fassara ne. Hadin kai da zamantakewar Najeriya dunkulalliyar kasa daya shine gabadayan mu muka saka a gaba tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Share.

game da Author