JAMB za ta bayyana ranakun da jami’o’in kasar nan za su fara daukan sabbin dalibai

0

Hukumar shirya jarabawar shiga jami’oin kasar nan, JAMB ta ce za ta bayyana ranakun da jami’o’i za su fara daukan sabbin dalibai a kasar nan.

A baya, hukumar ta tsaida ranar 21 ga watan Agusta ranar da jami’o’in kasarnan za su fara daukan sabbin dalibai.

A wata takarda da JAMB ta rabawa manema labarai ranar Lahadi, kakakin hukumar Fabian Benjamin ya ce hukumar za ta gana da shugabannin jami’o’in kasar nan domin a samu matsaya daya kafin ta bayyana ranakun.

An samu wannan canji ne a bisa dalilin matsalolin da aka fada ciki saboda Korona da kuma rashin yin jarabawar kammala salandare da daliban ajin karshe na makarantu basu yi ba.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya Ma’aikatar Ilimi ta bayyana ranakun da daliban ajin Karshe za su rubuta jarabawar kammala karatu.

Ma’aikatar ta shaida cewa gaba daya kaf za a kammala jarabawa a makarantun kasar nan a watan Nuwamba.

Karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajuiba ya sanar da haka bayan ya kammala zama da shugabannin hukumomin jarabawar ajin karshe da ya yi a Abuja.

Ga yadda aka tsara:

1. Za a fara rubuta jarabawar NABTEB ranar 21 ga Satumba a kammala ranar 15 Oktoba.

2. Jarabawar NECO da yan ajin karshe na babban sakandare ke zanawa za gudana ne daga ranar 5 ga Oktoba zuwa ranar 18 ga Nuwanba.

3. Za a rubuta jarabawar NECO na ‘yan ajin karshe na karamar Sakandare JSS 3 ranar 24 ga Agusta sannan a kammala ranar 7 ga Satumba.

4. Jarabawar shiga makarantun sakandare da ‘yan aji shida na makarantun firamare ke rubutawa wato NCEE za a rubuta ranar 17 ga Oktoba na 2020.

5. Za a kammala rajistan jarabawar NECO da ake yi yanzu rana 10 ga watan Satumba 2020 sannan ma’aikatar ilimi ta ce ba za a kara kwanaki ba.

6. Za a rubuta jarabawar NBAIS ranar 23 ga Satumba a kammala ranar 17 ga Oktoba.

Ministan ilimi Nwajuiba ya umurci duk hukumomin rubuta jarabawar da su gaggauta fidda jadawalin Jarabawar su nan da mako daya.

Ya kuma ce dole ne dalibai su zo wurin rubuta jarabawar da takunkumin fuska da man tsaftace hannu.

Share.

game da Author