Gwamnatin jihar Ogun ta bayyana cewa samun dabarun yin tsarin bada tazarar iyali a jihar ya ragu matuka.
A dalilin haka jihar za ta yi fama da matsalolin samun yawan mata da za su rika samun ciki da ba a so da yawa-yawan zubar da ciki.
Jaridar ‘BusinessDay’ ta wallafa rahotan haka batan wani bincike da ta yi a wasu kananan hukumomi 20 dake jihar.
Sakamakon binciken ya nuna cewa wannan matsala na da alaka da karancin ma’aikatan lafiya da bullar annobar Korona.
Idan ba a manta ba Sakamakon binciken da kungiya mai zaman kanta ‘Family Planning 2020 (FP2020)’ ta gudanar ya nuna cewa akalla mata miliyan 6.5 ne ke amfani da dabarun bada tazaran iyali a Najeriya.
Binciken ya nuna cewa an samu karuwar yawan mata da ke amfani da dabarun bada tazarar iyali a wasu kasashen duniya masu tasowa guda 68.
Shugaban kungiyar Beth Schlachter ta bayyana cewa an samu ci gaba a kasashen duniyan da suka hada kawance da su musamman Najeriya.
Schlachter ta ce binciken da suka gudanar a Najeriya ya nuna cewa a dalilin amfani da dabarun bada tazarar iyali mata akalla miliyan 2.3 basu daukar cikin da ba su so ba. Sannan a wannan shekara na 2019 an samu karin mata miliyan 9 da ke amfani da dabarun tsara iyali.
Ta kuma ce hakan ya sa an samu nasarar hana mata 800,000 zubar da ciki musamman ta hanyoyin da basu dace ba, sannan a shekarar 2018 an ceto rayukan mata 13,000 a wajen haihuwa.
Discussion about this post