SUNAYE: El-Rufai ya yi sabbin nade-nade a manyan ma’aikatun gwamnatin jihar

0

Gwamna jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi sabbin nade-nade a wasu Ma’aikatun jihar.

A cikin wata takarda da mai ba gwamnan shawara kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye ya fitar ranar Litini, El-Rufai ya nada sabbun Darektoci da babban sakataren Hukumar Tara Haraji Ta jihar Kaduna.

Wadanda aka nada suna hada da;

El-Rufai ya Jeremiah Adams, Mohammed Lawal da Simeon Kato a matsayin manyan Darektocin Hukumar KADIRS, sannan an nada Aysha Mohammed a matsayin sakatariya kuma mai ba hukumar shawara kan harkokin shari’a.

Haka kuma an nada Ishaya Anka, shugaban Ma’aikatar Kula da Kananan Hukumomin Jihar.

Sannan an nada,  Magaji Sadiq, Mahmud Zailani da Cecilia Musa are a matsayin mambobi na dindindin, da za su wakilci shiyoyyin jihar Uku.
An nada Dan shugaban hukumar Fansho ta jihar ita kuma Salamatu Isah an nada babban sakatariyar hukumar.

An nada Dr Zayyad Tsiga babban sakataren Hukumar Rajistan ‘yan jiha shi kuma Abdullahi Bayero, Janar Manaja na Hukumar Bunkasa Ayyukan Gona ta Jiha sanan gwamna El-Rufai ya nada Usman Danbaba a matsayin mai taimaka masa.

Haka kuma, Gwamna El-Rufai ya nada Suleiman Tahir a matsayin shugaban raya Kamfanonin da masana’antu da bada kananan basuka ta jihar, shi kuma Mustapha Shittu babban Sakataren hukumar.

Share.

game da Author