Da karfin Gwamnatin Tarayya za mu ci zaben gwamnan Ondo -Jigon APC

0

Wani jigon jam’iyyar APC a Jihar Ondo, Isaac Kekemeke, ya yi barazanar cewa jam’iyyar APC mai mulki za ta yi amfani da karfin mulki na Gwamnatin Tarayya domin ta lashe zaben gwamnan jihar Ondo.

Za a gudanar da zaben gwamnan jihar Ondo a ranar 10 Ga Oktoba, bayan an gudanar da zaben gwamnan jihar Edo a ranar 19 Ga Satumba, duk a cikin shekarar 2029 din nan.

Kekemeke na daya daga cikin ‘yan takarar da suka yi kokawar neman takara a zaben fidda-gwani tare da Gwamna Rotimi Akeredolu, kuma ya taba yin shugabancin APC a jihar Ondo.

Sahara Reporters ce ta fara nuno Kekemeke ya na jawabi ga wasu magoya bayan APC a cikin wani bidiyon da yanzu haka fallasa. Ya kara da cewa ya su bi duk irin hanya da za su iya bi domin su ci zabe.

Kekemeke ya kuma bugi kirji tare da yin kirarin cewa ‘yan-ta-kifen APC ne suka kekketa fastar Eyitayo Jegede, dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP na jihar Ondo.

“Za mu yi amfani da dukkan masu goyon bayan jam’iyar APC domin su ci zaben gwamnan da za a yi cikin watan Oktoba mai zuwa.

“Eyitayo Jegede ai kukan-dadi ya ke yi, da ya ke cewa an kekketa fastocin sa na PDP na takarar gwamna. Ai bai ma fara ganin ‘tsiya da rashin mutunci’ ba tukunna.

“Yanzu fa Gwamna Akeredolu ne kadai ke fafatawa da shi. Yayin da aka ce Gwamnatin Tarayya ta shigo cikin nan da karfin ta, ai Jegede tserewa zai yi da kafar sa. Yahaya Bello ma ya fi karfin sa, ballantana ni. Ni fa cikakken tantirin takadarin Neja Delta ne. Don haka mun san kan tsiyar da za mu kulla irin tsiyar da ake kullawa a ci zabe.”

A cikin bidiyon ya ce, za su yi duk yadda za su yi domin su mamaye zaben a dukkan kananan hukumomi domin su lashe ko’ina, su hana Jegede na PDP samun komai.

Haka Kekemeke ya fada a cikin bidiyon.

Ya ki amsa kiran da PREMIUM TIMES ta yi masa domin ta ji karin bayanin abin da ya ke nufi.

Share.

game da Author