Ministan Tsaro Bashir Magashi, ya kara jaddada niyyar sa ta sauya fasali da alkiblar tsaron kasar nan, domin magance babban kalubalen matsalar tsaron da kasar nan ke fuskanta.
Kakakin Yada Labarai na Ministan Tsaro, Muhammad Abdulkadiri ne ya sanar da haka cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar, domin tunawa da cikar ministan shekara daya da nadawa minista.
Magashi ya kuma kara jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da kara inganta karfin tsaron kasar nan wanda zai kara karfafa wanzar da zaman lafiya da tsaron kasa baki daya.
Ya gode wa Shugaba Muhammadu Buhari da ya ba shi damar sake bauta wa kasar sa. Ya ce ya na kan wannan gagarimin aikin da aka ba shi ya na yi nan da shekaru masu zuwa.
Ya jinjina wa Buhari dangane da irin gagarimin goyon bayan da ya ke bai wa Sojojin Najeriya wajen ganin an magance ta’addanci da kuma matsalar ‘yan bindiga da sauran kalubalen rashin tsaro a kasar nan.
Minista Magashi ya sha alwashin cewa wannan matsalar tsaro wata rana za ta zama abin bada tarihi,
Magashi ya umarci Manyan Hafsunan Hafsoshin Najeriya da sauran shugabannin bangaren tsaro su ci gaba da jajircewar kara nuna kishin Najeriya, saboda maganar samar tsaro ta shafi kowa da kowa a kasar nan.