Tsohon gwamnan Jihar Imo, Ikedi Ohakim ya shiga cikin tsomomuwar bahallatsar rikici shi da wata farkar sa, yadda har sai da kaurewar da suka yi ta kai ‘yan sanda sun shiga tsakanin.
Ohakim ta kai shi ga yin rahoto ga jami’an ‘yan sanda cewa matar ta ci zarafin sa a dakin otel din sa a Abuja.
Matar mai suna Chinyere Amuchiewa, ita ma ‘yar asalin Jihar Imo ce, amma ta na sayar da kayan alatu a Legas.
Ohakim mai shekaru 63, ya yi gwamna a Jihar Imo daga 2007 zuwa 2011. Ya yi takarar sanata a 2019 amma aka kayar da shi a zabe.
Shi ke auren Chioma Ohakim, wata lauya har su na da ‘ya’ya biyar.
‘Kokawa a gaban ‘Yan Sanda:
Cikin wata takardar korafin da Ohakim ya aika wa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Adamu, a ranar 20 Ga Janairu, Ohakim ya bayyana cewa:
“Ranar 18 Ga Janairu, 2020, Chinyere ta keta min mutunci, yayin da ta yaudare ni zuwa taron ganawa da ita. Ni kuma sai na gayyace ta, na ce ta zo a hotel din da na ke ta same ni a daki, a BON Hotel, Asokoro. Kuma ta zo karfe 12:15 na rana tsaka.
“Bude kofar da na yi ke da wuya kawai sai ta cukumi riga ta, ta rike ni kam, sannan ta bangaje ni da karfin tsiya ”
Tsohon gwamnan ya ci gaba da cewa, “yayin da na yi taga-taga, na kusa faduwa amma na mike tsaye, sai Chinyere ta rarumi wayoyi na. Ni kuwa na bi ta muka rukume, na kwace wayoyin daga hannun ta. Nan sai na ga ta nufi jakar ka cikin sauri ta na neman fito da wani abu da na yi tsammanin bindiga ce.”
Ohakim ya ce ganin haka sai ya fice daga dakin otal din ya kururuwar neman taimako.
Ya shaida wa ‘yan sanda cewa idan suka binciki CCTV din otal din, za su ga bidiyon duk abin da ya faru.
Ya kara da cewa nan da nan sai ya shigar da korafi a ofishin DPO na Asokoro, Abuja.
Tsohon gwamnan ya shaida wa ‘yan sanda cewa Chinyere ‘yar shekara 56 ce, kuma ta taba yin aure.
Ya kuma kara da cewa Chinyere farkar sa ce, wadda ya rika daukar dawainiyar kashe mata makudan kudade, har ma ta yi ruwa da tsaki wajen sake takarar gwamna da ya yi cikin 2019.
Ya ce bayan nan ne dangantaka ta baci a tsakanin su, har ta ke ta yi masa barazanar kulla masa sharri da ikirarin gamawa da shi.
Ohakim ya ce ya firgita sosai, shi ya sa ya nemi Sufeto Janar ya shiga tsakanin su.
‘Yan Sanda su sa baki:
‘Yan sanda sun nemi ya kai musu shaidun da ya ce ya na da su da hujjoji a Ofishin CID a ranar 1 Ga Yuni.
Wani Kwamishinan ‘Yan Sanda mai suna Abdulkadir Jimoh ne ya sa wa wasikar da aka yi wa Ohakim hannu.
Ohakim da farkar ta sa sun amsa kira a Hedikwatar ‘Yan Sanda, inda wani Mataimakin Sufeto Janar ya yi masu tambayoyi. AIG din shi ne Shugaban Bangaren Binciken Kwakwaf da Leken Asiri.
Ganawar PREMIUM TIMES Da Chinyere:
Chinyere ta shaida wa wakilin PREMIUM TIMES cewa Ohakim bai bayar da wata hujja ko daya a kanta a hannun ‘yan sanda ba.
Kokarin da PREMIUM TIMES ta yi domin jin ta bakin Ohakim ko kanin sa Emmanuel ya ci tura. Saboda sun ki daukar waya, kuma ko tes aka tura masu, ba su rubuto amsa su aiko.
Sai dai da PREMIUM TIMES ta tambayi Chinyere zargin Ohakim na neman ta, cewa kwarai, sun yi nema a tsakanin su ita da tsohon gwamnan.
“Ni fa ba karamar yarinya ba ce. Da ni farkar sa ce. Kuma ina da ‘yancin da zan nemi duk namijin da na ga dama.” Haka ta rufe bakin wakilin PREMIUM TIMES lokacin da ta fahimci ya cika ta da tambayoyi.
Amma kuma kafin a zo nan, ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa rikicin na su ba wani abu ba ne, a kan kudin ta ne da tsohon gwamnan ya karba ya ki biyan ta.
Ta yi Ikirarin cewa Ohakim ya je har kantin ta a Lagos ya kwashe akwatai, jikuna, takalma duk na alatu da sauran kayayyaki masu dan karen tsada. Kuma har yau ya ki biyan ta.
Sai dai kuma a cikin korafin da ya aika wa Sufeto Janar, Ohakim ya ce duk kyauta ta ba shi wadannan kayan na alatu.
“Ba a lokacin ta taba yi min kyauta ba. Sau biyu ko sau uku ta na fita waje, ta na dawo min da tsarabar kofi, turare, jaka, har da riga.”
Ya ce shi ma ya sha yi mata kyaututtuka, shi ya sa ita ma ta rika yi masa.
“Karya ya ke yi, duk abin da ya lissafa, bashi ya dauka, ba kyauta na ba shi ba.” Inji Chinyere, a hirar ta da PREMIUM TIMES.
“Na sha tambayar sa ya na kin biya na. Akwai wata rana dai har na tambaye shi, na ce, “shin wai kai wane aiki ka ke yi a rayuwar ka yanzu? Ranar da na gane cewa dan damfara ne, ita ce ranar da ya turo min kalamin muryar sa da ya yi rikodin, ya ce ya dauke min dala 200,000.”
Chinyere ta turo wannan muryar ga PREMIUM TIMES, Kuma mun saurare ta. Sai dai ba mu tantance shin muryar Ohakim ce ko ta wani ce ba.
‘Kokawa A dakin Otal da Ohakim’:
Chinyere ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa karya Ohakim ke yi, ba ta cukume shi ko yi wata kokawa da shi ba.
Ta ce shi ya ce ta same shi a otal, kuma ta je, tsammanin kudin da ta ke bin sa zai biya ta.
Ta ce ya sha yaudarar ta da damfarar ta. “Har zoben jabu ya taba makala min a tsaya, na karya, wai zai aure ni.” Inji Chinyere.