Gungun mahara dauke da muggan makamai sun yi wa tsohon kwamishina a Zamfara takakkiya har gida, suka arce da ‘ya’yan sa biyu da kuma wani jami’in tsaron da na NSCDC.
Da ya ke tabbatar da afkuwar mummunan lamarin a sanarwar manema labarai, kakakin yada labarai na Rundunar ‘Yan Sandan Zamfara, Muhammad Shehu, ta tabbatar da cewa an arce da ‘ya’yan Bello Dankande, tsohon Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu tare da kashe wani mutum daya da jikkata wani kafin su gudu da ‘ya’yan su biyu.
Ya ce dandazon ‘yan bindiga sun yi wa gidan sa tsinke misalin karfe 4:30 na yammacin ranar Talata, a kauyen Gamji cikin Karamar Hukumar Bakura.
“Wajen karfe 4:30 na yammacin ta yau Talata ne mahara suka je har gida suka arce da ‘ya’yan tsohon kwamishinan biyu, sannan kuma sun kashe wani mutum daya, suka kuma jikkata wani daya shi ma.
“Maharan sun tafi da wanj jami’in tsaron NSCDC da ke gadi a gidan tsohon kwamishinan.
“Amma dai Rundunar ‘Yan Sanda ta baza zaratan jami’an ta, domin gano duk wani lungun da aka gudu da su don su kubutar da suda ran su.
“Mu na tabbatar wa tsohon kwamishinan cewa jami’an mu za su ceto yaran sa, kamar yadda suka ceto mutanen nan shida, ciki har da hakiman Basasa da Ruwan Guzo da aka arce da su daga garuruwan cikin Karamar Hukumar Takata Mafara da Bakura.
Ya gargadi jama’a su daina zakewa wajen gaggawar yin fito-na-fito da mahara a irin wannan harin idan sun mamaye wani gida ki kauye.
Ya ce a rika yin gaggawa ana sanar da jami’an tsaro.
Discussion about this post