Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi na Ekiti ya ce gwamnoni sun goyi bayan a bai wa tsarin shari’a cin gashin kan su. Sai dai kuma ya ce sun fi damuwa a kan yadda za a aiwatar da kuma tafiyar da tsarin.
Kayode ya yi wannan bayani a Ado Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, ranar Litinin a lokacin da ya karbi bakuncin sabon Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta kasa (NBA), Olumide Akpata a ofishin sa da ke Gidan Gwamnati.
Fayemi ya ce ya jagoranci tawagar gwamnoni a madadin sauran Gwamnonin Najeriya, inda suka kai ziyarar ganawa da Shugaban Alkalan Najeriya, Tanko Muhammad da kuma wurin Shugabar Alkalan Kotunan Daukaka Kara, Monica Dongban-Mensem dangane da batun bai wa fannin shari’a da alkalai cin gashin kai a jihohi.
Ya ce ganawar ta maida hankali ne wajen cimma matsaya a kan irin hanyoyin da bangaren shari’a din zai rika gudanar da ayyukan sa a wannan sabon tsarin cin gashin kai, a kowace jiha.
Ya ce gwamnoni sun yi amanna da kuma yakinin cewa yi wa bangaren shari’a garambawul shi ne zai kara nagartar tsarin dimokradiyya. Don haka tilas ne a aiwatar da tsarin a bisa yadda dokar kasa ta tanadar.
“Abu guda da ya kamata a sani shi ne wannan batun cin gashin kan bangaren shari’a a jihohi ya na da muhimmanci ga gwamnoni matuka.
“Dukkan gwamnonin Najeriya na goyon bayan a bai wa bangaren tsaro kason cin gashin kan su.
“Mu na kallon cin gashin kan bangaren shari’a babban ginshikin nagartar dimokradiyya ne. Don haka tilas ne mu ba shi goyon bayan ganin ya tabbata.
Daga nan sai gwamnan ya roki Shugaban Kungiyar Lauyoyi ya ja lauyoyin Jihar Ekiti a jiki, domin a rika damawa da su a harkokin shari’a a kasar nan.
A nasa jawabin, Akpata ya sha alwashin kawo gagarimin canji a cikin tafiyar Kungiyar Lauyoyi ta Kasa.
Discussion about this post