ZABEN EDO: Tsakanin Ganduje da Wike, wanda ya raba fada bai yi kallo ba

0

Nada Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano da APC ta yi, a matsayin Shugaban Yakin Cin Zaben Gwamnan Jihar Edo, bai ba masu nazarin yadda siyasar Najeriya ta sauya tun daga zaben 2019 mamaki ba.

Ganin haka, sai ita ma jam’iyyar PDP ta nada Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas Shugaban Kamfen din Cin Zaben Gwamnan Jihar Edo.

Yayin da APC ke ganin ko ana ha-maza-ha-mata sai ta rike kujerar ta, duk kuwa da cewa wanda ke kai, Gwamna Godwin Obaseki ya koma PDP, kuma shi ne dan takarar ta.

Ita kuwa PDP na ganin ko ana-muzuru-ana-shaho, sai Obasaki ya zarce, amma a wannan karo na biyu, a karkashin tutar PDP.

Wike Da Ganduje: Kowane Gogarma Da Ranar Sa

Ganduje, Tsoho Mai Daka Wa Yaro Kashi:

Ganduje ya yi kaurin suna tun daga yadda manyan mukarraban jagaliyar sa suka damalmala zaben gwamna a Mazabar Gama, cikin Karamar Hukumar Nasarawa a zaben 2019.

Kakudubar da ta faru da karankatakaliyar bayyana zaben cewa bai kammalu ba, ya bai wa Ganduje yin nasara a ranar da aka maimaita, duk kuwa da cewa a zaben farko an dan takarar PDP Abba Gida-gida ya tsere masa da sama da kuri’u 27,000.

Duk da duniya ta shaida yadda matasa ‘yan-ta-kife suka rika fatattaka da ragarhazar masu adawa da Ganduje a ranar zaben ‘inconclusive’, an bayyana cewa an gudanar da zaben lami lafiya, duk da cewa cikin wadanda kasar nan ta tabbatar an fatattaka, har da ‘yan jarida.

A lokacin zaben, duk wani makamin gargajiya da ka sani, an rika yawo da shi tsirara ana bin masu adawa.

Baya ga cewa an sas-sari da dama, a cikin birni da kauyuka ‘yan adawa da dama sun kaurace wa zaben saboda gudun kada a sas-sare su a zaben na ‘inconclusive’, yadda a wasu wurare ko kuri’a daya PDP ba ta samu ba.

Ganduje ya samu nasarar zarcewa karo na biyu, a zaben da har abada dimbin jama’a da dama, musamman wadanda abin ya faru a idon su, ba za su taba amicewa an gudanar da sahihin zabe ba.

Ganin yadda Ganduje ya hana idanun sa da na ‘yan adawa barci, har sai da ya ciwo zaben 2019 a abin da jama’a suka rika kira “Aikin Gama ya gama”, ba abin mamaki ba ne don ya jagoranci rundunar cin zaben Gwamnan Edo na APC.

Shi da kan sa a wani jawabi da ya yi wa manema labarai a Gidan Gwamnatin Kano, bayan Osagie Ize-Iyamu ya zama dan takarar APC na zaben Edo, Ganduje ya ce, ” Jihar Kano za ta yi duk abin da za ta iya domin APC ta yi nasara a zaben Edo.”

Wike, Karen Bana Maganin Zomon Bana:

Bahaushe ya yi gaskiya da karin maganar sa mai cewa, “rike mahaukacin ka, don ya yi maka maganin mahaukacin wani.”

Wike ya kuma zama ‘na kawo karfi ya fi an girme ni.’ Ya zama ‘ko dubu ta ta taru’. Kai Wike ya zama, ‘an buga da kai an bar ka.’

A zaben 2019, a jihar Ribas an yi gwagwagwa, an yi gumurzu, kuma an shirya wa Wike tuggu, amma sai da ya tsallake, duk da cewa shi kadai ke yakin sa. Ba shi da kwamanda, ba shi da runduna ballantana ayarin mahara. Shi kadai ya ke tunkarar filin daga, tamkar Iliya Dan Maikarfi.

Irin yadda Wike ya rika kafsa rikici da sojoji a zaben ribas, dole ya zame wa masu adawa da shi

Karon Gwangwa Da Gwangwa:

Tabbas babu wanda ya dace daga bangaren PDP ya tunkari rundunar Ganduje, sai Nyesom Wike, domin idan takamar ka daura banten-bakin-biri a yakin siyasa, Wike wani Wargaji ne, wanda sai dai warkin maraki ke iya rufe masa katara.

Duk da har yanzu ba mu ji sunayen kwamandojin da ke cikin rundunar Wike ba, baya ga mataimakin sa Gwamna Umar Pintiri na Adamawa, zaratan da ke karkashin Ganduje sun sa kowa na ganin cewa APC ta fito ne bakin-rai-bakin-fama. Godswill Akpabio, Timipre Sylva, Hope Uzodinma da sauran wasu karta-kartan da APC ke takama da su, duk suna cikin rundunar Ganduje.

Zaben Edo Zai Kasance Ma’aunin Darajar Dimokradiyyar Najeriya:

Hakika da dama na nuna damuwa yadda bangarorin biyu ke neman ko ta halin kaka sun kwaci kujerar gwamnan Edo.

A wannan lokaci na annobar Coronavirus, inda jama’a da dama kaurace wa zaben za su yi, zai iya yiwuwa ta kasance cewa jama’a sun kaurace, an bar bangarori biyu na rundunar APC da PDP su gwada karfi a kan akwatun zabe, a cibiyar tattara sakamako da kuma wurin bayyana sakamako.

A irin wannan yaki na ‘katilan-makatulan’ me talaka zai ce? Sai dai ya ce, ‘wanda ya raba fada bai kallo ba!”

Share.

game da Author