Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 454 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Juma’a.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum Lagos – 87, Edo – 63, FCT – 60, Ondo – 41, Benue – 32, Abia – 31, Ogun – 29, Oyo – 19, Kaduna – 17, Delta – 16, Enugu – 15, Borno – 14, Plateau – 9, Nasarawa – 8, Kano – 5, Bauchi – 4, Gombe – 2, Katsina – 1 da Kogi – 1.
Yanzu mutum 27, 546 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 11,069 sun warke, 628 sun rasu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum, 10, 910, followed by FCT – 2, 080, Oyo – 1, 451, Kano – 1, 262, Edo – 1, 269, Delta – 1, 165, Rivers – 1, 114, Ogun –927, Kaduna – 835, Katsina – 579, Bauchi – 516, Gombe – 513, Borno – 515, Ebonyi – 483, Plateau – 402, Ondo – 394, Imo – 352, Abia – 482, Enugu – 357, Jigawa – 318, Kwara – 369, Bayelsa – 324, Nasarawa – 221, Sokoto – 152, Osun – 148, Niger – 116, Akwa Ibom – 104, Adamawa – 89, Kebbi – 81, Zamfara – 76, Anambra – 73, Benue – 97, Yobe – 61, Ekiti – 43, Taraba – 19 and Kogi – 5.
Idan ba a manta ba, a ranar Talata, kungiyar kiwon Lafiya ta duniya (WHO), ta bayyana cewa yanzu ne duniya za ta afka cikin babban bala’in Coronavirus.
Shugaban WHO, Tedros Ghebreyesus ya fitar ya ce a baya ba a ga komai ba tukunna.
Tedros wanda aka buga bayanin sa a BBC da rumbun tattara bayanan kamuwa da kisan adadin mutane sakamakon Coronavirus, wato worldometers.org suka wallafa, ya ce matsawar gwamnatocin kasashen duniya ba su gaggauta tashi tsaye sun yi da gaske ba, to wannan cuta za ta yi wa duniya rundugun da ya wuce wanda ake ciki a yanzu fiye da kima.
Discussion about this post