Gwamnan Ebonyi, David Umahi ya kamu da Korona

0

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya kamu da Korona.

Gwamna Umahi ya bayyana haka a wata takarda da ya da ya saka wa hannu ranar Asabar.

Ya ce ya mika ragamar mulkin Ebonyi ga matamakin sa Kelechi Igwe.

Bayan haka ya umarci duka jami’an gwamnati dake aiki a fadar gwamnati su garzaya cibiyar yin gwajin Korona a jihar a dibi jinin su.

Umahi ya shiga cikin jerin gwamnonin da suka kamu da cutar a Najeriya.

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammaed wadda shine gwamna na farko da ya kamu da cuta, Sai gwamnan Kaduna Nasir El-rufai, Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, Na Delta, Ifeanyi Okowa da gwamnan Abia Ikpezua.

Share.

game da Author