Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Kaduna ya angwance

0

A karshen wannan mako ne shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Kaduna, Muhammed Sani Abdullahi ya auri Amaryar sa Maryam Lawal, a birnin Kano.

An daura auren Mohammed Sani da Amaryar sa Maryam a masallacin Umar Farouq dake Titin UDB a birnin Kano.

Mohammed Sani wanda shine kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na jihar tun daga 2015 zuwa 2019, na daga cikin nangaban goshin gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai

Bayan nasara da Nasir El-Rufai yayi a zaben 2019, sai ya nada Mohammed Sani shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Kaduna.

Baya ga ‘yan uwa da abokan arziki da suka halarci bukin a birnin Kano, masu sarauta daga masarautar Lere sun halarci bukin dan uwan su Mohammed Sani.

Ciki akwai Dan Lawal din Lere, Dan Amar, Majikiran Sarkin Lere, Dan Iyan Lere da dai sauran su.

Allah ya bada zaman Lafiya, Amin.

Share.

game da Author