Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 571 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Lahadi.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 152, Ebonyi 108, Edo 53, Ondo 46, FCT 38, Oyo 20, Kwara 19, Filato 17, Osun 14, Bayelsa 14, Ekiti 14, Katsina 14, Akwa Ibom 11, Kaduna 11, Rivers 11, Niger 10, Ogun 7, Kano 6, Cross River 4 da Bauchi 2.
Yanzu mutum 32, 558 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 13, 447 sun warke, 740 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 18,371 ke dauke da cutar a Najeriya.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 12,427, FCT – 2,576, Oyo – 1,706, Edo – 1,731, Delta – 1,359, Rivers – 1,368, Kano – 1,309, Ogun – 1,087, Kaduna – 989, Katsina – 1,726, Ondo – 716, Borno – 586, Gombe – 530, Bauchi – 521, Ebonyi – 616, Filato – 533, Enugu – 476, Abia – 405, Imo – 386, Jigawa – 321, Kwara – 330, Bayelsa – 313, Nasarawa – 244, Osun – 245, Sokoto – 153, Niger – 145, Akwa Ibom – 145, Benue – 121, Adamawa – 110, Anambra – 93, Kebbi – 86, Zamfara – 76, Yobe – 62, Ekiti – 63, Taraba- 27, Kogi – 5, da Cross River – 9.
Wasu abinci da ke kara karfin garkuwar jiki:
Wasu kwararrun likitoci dake a kasar UK sun shaida cewa sinadarin ‘Vitamin D’ baya warkar da cutar coronavirus.
Likitoci sun fadi haka ne ganin yadda wasu mutane ke fadin cewa sinadarin ‘Vitamin D’ na da ingancin warkar da cutar coronavirus.
Sinadarin ‘Vitamin D’ na kara karfin kashi, inganta karfin garkuwan jiki sannan yana kare mutum daga kamuwa da cututtukan dake sa a samu matsalar toshewar numfashi, kuma wara na da wannan sanadari.
A dalilin haka likitoci ke Kira ga mutane da su rika cin abinci dake dauke da sinadarin ‘Vitamin D’ domin inganta garkuwar jikinsu amma ba domin su kare kansu daga kamuwa da cutar coronavirus ba.
Abincin dake dauke da sinadarin Vitamin D sun hada da:
1. Dafaffen kwai
2. Lemun Zaki
3. Hanta dafaffe ko Kuma soyayye
4. Kifi
5. Madara
6. Madaran waken soya
7. Wara
8. Kubewa
Virus-free. www.avast.com
Discussion about this post