Kada a salaka suna na cikin binciken harkallar Magu – Osinbajo ga Sufeto Janar

0

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya gargadi masu yin binciken shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu da su shiga taitayin su bisa kokakain cusa sunan sa cikin harkallar binciken tsohon shugaban EFCC din.

Jaridar Pointblank, mallakin wani tsohon hadimin tsohon shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ya wallafa cewa Ibrahim Magu ya waske da dala Naira 39 cikin kudaden da ya ke kwatowa wurin barayin gwamnati, kuma ya damka ya mataimakin shugaban Kasa Osinbajo naira biliyan hudu toshiyar baki.

A cikin wannan rahoto, an rubuta cewa Magu ya aikawa mataimakin shugaban Kasa naira biliyan hudu, a ranar da shugaba Buhari ya fice kasar nan zuwa kasar Birtaniya.

A dalilin haka, mataimakin shugaban Kasa, ta hannun lauyan sa ya karyata wannan zargi inda ya shaida cewa babu abinda ya hada shi da karbar toshiya daga Magu, maganan da ake yi ta kazon kurege ce kawai.

Baya ga haka, ya aika wannan wasika ga ministan Shari’ar Najeriya, Abubakar Malami, da sufeto Janar din Najeriya, Mohammed Adamu

Karanta Labarin mu na baya:

Da misalin karfe 7:30 na yammacin Talata, Jam’ian tsaro suka dira gidan shugaban hukumar EFCC da aka dakatar, Ibrahim Magu, inda suka gudanar da bincike.

Daya daga cikin masu gadin gidan ya tabbatar wa Premium Times cewa jami’an tsaron sun dira gidan Magu dake Maitama da kuma gidan sa na kan sa dake Karu.

Ya kara da cewa bayan sun gama binciken gidan, sako sako, daki dai, kurdi-kurdi sai suka fito suka ba da takar da muka sa hannu.

” Ba su tafi da komai ba.”

Share.

game da Author