ZAMAN KOTU: EFCC ta kasa nuna cin hancin $25,000 da take zargin Shehu Sani ya karba daga ASD

0

A ci gaba da zaman kotu dake shari’ar zargin karbar cin hancin da ake tuhumar tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya Shehu Sani yayi, hukumar EFCC da ta maka sanatan a Kotu ta kasa mika shaidun da ta dogara akai cewa lallai an ba Sani dauda, ASD ya ba sanata Shehu Sani $25,000 don cin hanci ga shugaban hukumar, Ibrahim Magu.

Ko da alkalin kotun ya bukaci EFCC ta mika shaidar an bada wannan kudi kuma wanda ake tuhuma ya karbi kudin, har ya dawo mata da su, sai hukumar ta ce, ayya, ai bata tare da wannan kudi yanzu. Cewa duka irin wadannan kudade sukan kai su ajiya ne babban bankin kasa, wato CBN.

Lauyan EFCC ya bukaci a dage shari’ar zuwa har EFCC ta karbo kudaden daga CBN domin bayyana shi a kotu.

Alkalin kotun ya dage shari’ar zuwa ranakun 19, 20, 21, da 22 ga watan Oktoba.

Sai dai kuma lauya mai kare wanda ake kara, wato lauyan sanata Shehu Sani yce lallai hukumar EFCC bata kware a aikin ta ba, saboda ko, yaya zata shiga kotu da mutum sannan kuma ta kasa bayyana shaidun da ake bukata a gaban alkali.

Ya ce ta san bata shirya bane za ta bari ana ta kai komo.

Idan ba a manta ba dan Sani Dauda (ASD Motors), mai suna Mohammed Dauda, ya shaida wa Kotun, shi shaida ne mahaifin sa ya damka wa Sanata Shehu Sani kudin da ya maida wa EFCC a matsayin shaida.

Mohammed ya yi wannan ikirari a lokacin da lauyan Shehu Sani ke masa tambayoyi a kotun, wadda ake ci gaba da tuhumar sanatan da laifin zamba.

Lauyan mai suna Abdul Ibrahim, ya tambayi Mohammed ko ya na a wurin lokacin da ake tattauna batun bayar da kudaden, sai ya ce shi dai a gaban sa mahaifin sa ya damka wa EFCC kudaden da Sani ya maida a matsayin shaida.

Daga nan sai dan na ASD ya ce ba shi da wata masaniyar ko mahaifin sa na da matsala da EFCC.

Tun da farko da lauya mai gabatar da kara Abba Mohammed ke masa tambayoyi, dan na ASD ya ce Shehu Sani ya hadu da mahaifin sa cikin watan Nuwamba, 2019.

Wannan mai bada shaida ya ce Shehu Sani ya shaida wa mahaifin sa cewa Babban Jojin Najeriya ta na yi wa wadanda suka shiga tsomomuwa alfarma. Don haka ma ya na nan ya na yi wa ASD alfarmar.

Ya ce idan zai samu wani dan ihisani aka bai wa Cif Jojin, to zai ji dadi sosai.

Mohammed ya ci gaba da shaida wa kotu cewa, tun daga lokacin da Shehu Sani ya karbi kudin, mahaifin sa bai sake jin komai daga gare shi ba.

Sannan kuma tsohon sanatan ba ya amsa kira idan mahaifin Mohammed din, wato ASD Motors ya kira shi. Kuma shi bai sake kiran sa ba.

Mai bada shaida ya ce sai lokacin da Shehu Sani ya ji mahaifin sa ya kai rahoto EFCC, sannan ya kira shi, a ranar da mahaifin nawa ya dawo daga aikin Hajji.

“Shehu Sani ya ce wa mahaifi na, da na san ka dawo, ai da na maido maka da kudin ka.”

“Dama kuma EFCC sun ba mu shawara cewa duk maganar da za mu yi ta waya da Shehu Sani ko gaba-da-gaba, to mu rika rikodin din ta.”

Ya tabbatar cewa kudin da mahaifin sa ya damka wa EFCC har dala 25,000.00, wadanda Shehu Sani ya maida masa ne.

It’s ma Fatima Umar, mai binciken tantance bayanan gaskiya da na boge a na’urar zamani, ta shaida wa kotu cewa muryoyin da suka kwasa suka saurara a wayoyin bangarorin biyu, na Shehu Sani ne da kuma ASD Motors, wanda ya kai karar Shehu.

An dai dage sauraren karar zuwa 9 Ga Yuli.

Share.

game da Author