Kabilar Igbo na farin ciki da alfahari da Buhari -Inji Athur Eze

0

Wani hamshakin dan kasuwa mai suna Athur Eze, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna soyayyar sa da kauna ga yankin Kudu maso Kudu (shiyyar kabilar Igbo), ta yadda ya ke bunkasa yankin da manyan ayyukan rayawa da inganta al’umma, tun bayan hawan sa mulki.

Eze ya yi wannan jawabi a wurin kaddamar da Shiyyar Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sanda ta 13, a Ukpo, cikin Karamar Hukumar Dunukofia, jihar Anambra.

Ya ce ya na matukar godiya ga Buhari da Manyan Jigogin Rundunar ‘Yan Sanda da har suka yi tunanin kafa Shir
yya ta 13 (Zone 13) a yankin sa.

“A yanzu haka Buhari na kan gyaran titin Enugu zuwa Anacha, ya na gina Gadar Kogin Neja ta biyu, kuma ya bada umarnin gina Shiyyar Rundunar ‘Yan Sanda ta 13 (AIG Zone 13) a cikin al’ummar yankin mu.” Inji Eze.

Ya ce tsakanin su da Buhari dai godiya buhu-,buhu.

“Mu kabilar Igbo mu na farin ciki da Shugaba Muhammadu Buhari, kuma za mu ci gaba da ba shi goyon baya wajen kokarin da ya ke ya na gina ayyukan bunkasa al’umma.”

Eze ya damka makullin ginin ga wakilin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Muhammed Adamu.

Sai dai kuma NAN ta ruwaito cewa babu gwamnonin yankin ko daya da ya halarci bikin kadddanar da ginin, sai sarakunan gargajiya na yankin da kuma ‘yan kasuwa.

Share.

game da Author