KWANTON-BAUNA: Boko Haram sun kashe zaratan sojoji 37

0

Akalla Zaratan Sojojin Musamman 37 ne Boko Haram suka kashe, a wani mummunan samamen kwanton-bauna da ‘yan ta’addar suka kai musu.

Kwakkwarar majiya ce ta tabbatar wa PREMIUM TIMES wannan mummunan al’amari da majiyar ta ce tun ranar Talata ya faru.

Majiyar ta ce an yi wa Zaratan Sojojin Musamman din kwanton-bauna ne a kan titin Maiduguri zuwa Damboa.

A ranar Laraba Rundunar Sojan Najeriya ta tabbatar da kai wa sojojin hari, amma suka ce mutum biyu kadai aka kashe.

Kodinatan Shirya Dabarun Yaki John Enenche, ya fitar da sanarwa cewa, “dakarun Najeriya sun yi kokari sun kubuta daga rintsin gumurzun Boko Haram, har ma suka kashe ‘yan ta’adda 17.”

Manjo Janar Enenche ya kara da cewa Boko Haram/ISWAP da dama sun tsere da munanan raunukan harbin bindiga.

A wani alayen da sosjoji suka saba yi, domin su bagarar da wani bala’i da ya afkar wa kasar nan, sai mahukuntan soja suka umarci Babban Kwamandan Operation Lafiya Dole ya tabbatar sojojin sa sun kwato titin Damboa zuwa Maiduguri.

Cikin makon da ya gabata ma sai da aka kashe soja 10 ciki har da wani Laftanar a wani harin kwanton-bauna.

Sai dai kuma ikirarin da Enenche ya yi cewa soja biyu kacal aka kashe, bai yi daidai da ikirarin da wasu sojojin da aka fafata yakin da su suka bayyana ba.

Wata majiyar da ta san komai dangane da abin da ya faru, ta ce mahukuntan soja na boye gaskiyar abin da ya faru ne kawai a kan harin da aka kai wa sojojin.

Majiyoyin PREMIUM TIMES wadanda duk sojojin da ke kan aiki ne, kuma masu masaniya da kusanci da wadanda ke bakin daga, sun ce “sojoji na boye abin da ya faru ne, su na binne gaskiyar lamarin a ksrkashin kasa.”

Wakilin PREMIUM TIMES ya ga mummunan hotunan tulin wasu gawarwakin sojojin da aka jibge cikin wani gida.

Yadda Boko Haram Suka Kai Wa Sojoji Farmaki:

* An kai musu farmakin ne a lokacin da zaratan sojoji daga bangarorin mayaka uku suka hada rundunar fita sintiri a kan titin Maiduguri zuwa Damboa.

“Kwatsam sai sojojin suka ci karo da gungun Boko Haram da ba a san adadin su ba, wadanda suka afka musu tsakanin kauyen Limanti da Bulabulin, kauyuka biyu da ke kusa da Damboa.”

Haka dai wata sahihiyar majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES.

*Dakarun Najeriya sun fafata gumurzun kokarin tsira daga kofar-raggon da Boko Haram suka yi musu.

*Amma Boko Haram sun ci gaba da sakar musu wuta, har sai da ta kai Kwamanda Kanar Bako ya yi kiran neman daukin gaggawa.”

“Bayan kura ta lafa, sojoji da yawa sun kwanta dama, wasu da yawa kuma ba a san inda suke ba.” Haka majiyar ta kara bayyanawa.

“A wurin gumurzun dai an kwashi gawarwakin sojoji 27, daga nan kuma aka kara gano wasu gawarwaki 10, inda suka cika 37 kenan.” Inji majiyar.

Majiyoyi sun kuma ce Boko Haram sun kwaci motocin harba manyan bindigogi samfurin tashi-gari-barde har guda hudu daga hannun sojoji.

PREMIUM TIMES ta gano cewa babu tabbacin sojojin Najeriya za su iya kubuta a duk lokacin da suka afka tarkon kwanton-,baunar Boko Haram.

PREMIUM TIMES ta tura wa Enenche da Kakakin Sojoji Sagir Musa adadin yawan sojojin da ta samu labarin an kashe, amma har yanzu ba su maido amsar sakon tes da aka yi musu ba.

Share.

game da Author