Gwamnatin jihar Legas ta tsaida da ranar 3 ga watan Agusta a matsayin ranar da za ta bude makarantu domin daliban dake aji 6 na firamare, ajin karshe na karamar sakandare JSS 3 da na karshe na babban sakandare SSS 3 su fara karatu.
Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya Sanar da haka ranar Juma’a yana mai cewa masu ruwa da tsaki a jihar ne suka yanke wannan hukunci na a bude makarantun waddana rukuinin dalibai kawai.
Sanwo-Olu ya ce kwamitin shugaban kasa Kan dakile yaduwar cutar covid-19 ta tsara wasu matakan guje wa kamuwa da cutar domin makarantun da za a bude su kiyaye domin kare lafiyar dalibai da malamai da za su dawo makaranta.
Ya ce gwamnati ta amince a bude makarantun ‘jeka ka dawo’ kawai banda na kwana.
Sanwo-Olu ya ce duk sauran makarantun za su ci gaba da daukan darasi ta yanar gizo.
Bayan haka gwamnan ya ce dokar hana taron mutane Sama da mutum 20 na aiki a jihar sannan dokar hana bude ofisoshi, kasuwani da wuraren shakatawa duk yana nan za su ci gaba da zama a rufe.
Sakamakon gwajin da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a ya nuna cewa mutum 10,639 ne suka kamu a jihar.
Mutum 2,681 sun warke sannan 177 sun mutu.
Discussion about this post