Asibitin koyarwa na jami’ar Calaba dake jihar Koros Ribas (UCTH) ta Sanar cewa mutum biyar sun kamu da cutar Korona a jihar.
Shugaban asibitin UCTH Ikpeme Ikpeme ya shaida cewa sakamakon gwajin cutar da aka yi wa wadannan mutane ne ya bayyana haka ranar Juma’a.
Ya ce an gudanar da gwajin cutar a wurin yin gwaji da hukumar NCDC ta amince da shi dake Abakaliki jihar Ebonyi.
Wannan shine Karo na biyu cikin mako daya da aka samu wadanda suka kamu da cutar a jihar.
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 626 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Alhamis.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum -193, FCT 85, Oyo 41, Edo 38, Kwara 34, Abia 31, Ogun 29, Ondo 28, Rivers 26, Osun 21, Akwa Ibom 18, Delta 18, Enugu 15, Kaduna 13, Filato 11, Barno 8, Bauchi 7, Adamawa 5, Gombe 4, Sokoto 1.
Yanzu mutum 27,110 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 10,801 sun warke, 616 sun rasu.
Idan ba a manta ba, a ranar Talata, kungiyar kiwon Lafiya ta duniya (WHO), ta bayyana cewa yanzu ne duniya za ta afka cikin babban bala’in Coronavirus.
Shugaban WHO, Tedros Ghebreyesus ya fitar ya ce a baya ba a ga komai ba tukunna.
Tedros wanda aka buga bayanin sa a BBC da rumbun tattara bayanan kamuwa da kisan adadin mutane sakamakon Coronavirus, wato worldometers.org suka wallafa, ya ce matsawar gwamnatocin kasashen duniya ba su gaggauta tashi tsaye sun yi da gaske ba, to wannan cuta za ta yi wa duniya rundugun da ya wuce wanda ake ciki a yanzu fiye da kima.
Discussion about this post