BINCIKEN-KWAKWAF: Yadda ake jidar bilyoyin nairori da sunan aikin titin jirgin kasa, daga zamanin Jonathan zuwa Buhari

0

Wannan fa wani labarin binciken-kwakwaf ne da mai karatu zai karanta, a kan yadda ake almubazzarantar da bilyoyin nairori a aikin gyaran titinan jirage. Amma kash, har yanzu ba a tsinana wani aikin da za a gani a yaba ba.

Yadda Gayyar Aikin Kwangilar Hanyar Jirgi Daga Fatakwal Zuwa Maiduguri Ta Watse

An yi wani kwarya-kwaryan taro a ranar 19 Ga Maris na wannan shekara a Abuja, tsakanin wasu jami’an Ma’aikatar Sufuri da Hukumar Kula da Jiragen Kasa, tare da wakilan wasu kamfanonin kwangila uku.

Ajandar taron dai guda daya ce tak – wato batun aikin kwangilar titin jirgin kasa daga Fatakwal zuwa Maiduguri ya shiririce gaba daya. A yanzu kuma gwamnati ta yanke shawarar kwace aikin kwangilar daga kamfanonin da aka baiwa, domin sake farfado da aikin.

Daraktan Ayyukan Jiragen Kasa na Ma’aikatar Sufuri, Mohammed Babakobi, ya nuna damuwa a lokacin taron wanda kuma shi ne shugaban taron, cewa tun cikin watan Maris, 2011 aka bayar da kwangilar, amma har yanzu ba a kammala ba, duk kuwa da dimbin kudaden da gwamnatin tarayya ta narka a aikin kwangilar.

Daga nan sai aka bai wa kamfanonin uku mako daya domin su je su rubuto bayanan daftarin yadda gwamnati za ta aiwatar da aikin titin jirgin.

Har yau PREMIUM TIMES ba ta samu daftarin yadda suka tsara za a gudanar da kwangilar ba.

Kamfanonin su ne: Eser W.A Limited, CGGC Global Project Nigeria Limited da kuma Lingo Nigeria Limited.

Titin Jirgi Daga Fatakwal Zuwa Maiduguri: Asali dai Turawan mulkin mallaka ne suka Gina titin tun kafin samun ‘yancin Najeriya a 1960.

Kafin ya lalace, ta kan titin ne aka rika bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin Kudu zuwa Arewa, kuma shi ne musabbabin bunkasar garin Kafanchan da Jos suka zama manyan garuruwa kuma cibiyoyin haka da harkokin ma’adinai.

Zamanin Mulkin Jonathan:

Ranar 10 Ga Maris, 2010 tun Goddluck Jonathan bai dade kan mulki ba, sai ya kaddamar da gagarimin shirin farfado da titin Jirgi daga Fatakwal zuwa Maiduguri. Aka raba aikin gida uku ga kamfanoni uku daban-daban.

An damka wani bangare daga Fatakwal zuwa Maiduguri ga kamfanin Eser W. A. LImited kan kudi naira bilyan 19.2.

Aka damka wa CGGC Global aikin gyaran daga Maiduguri zuwa Kuru akan kudi naira bilyan 24.5. Kamfanin Lingo kuma aka damka masa kwangilar aikin Kuru zuwa Maiduguri kan kudi naira bilyan 23.7.

An kuma ba su wa’adin watanni goma da watanni takwas su kammala aikin.

Shekaru 9 bayan kaddamar da kwangilar, aikin dai ya shiririce gaba daya. Babu aiki babu alamar sa, balle alamun kammalawa.

Aikin wanda aka bayar ga kamfanonin uku a kan kudi har naira bilyan 67.3, ba a san abin da aka ba su domin fara aikin ba. Amma dai an ce sun karbi makudan bilyoyin nairori.

Yanzu kuma jami’ai na kokarin zana hanyar da za a nemi mafitar al’amarin.

Inda Gizo Ke Saka:

PREMIUM TIMES ta shafe wata days cur ta na binciken wannan kwangiloli, kuma ta lura a bangaren da aka ba kamfanin Lingo Nigeria Limited nan ne aka fi fuskantar mummunar matsala. Saboda wakikin binciken kwakwaf na PREMIUM TIMES ya bi diddigin aikin tun daga Filato, Bauchi da Gombe.

Gogaraman dan siyasa Linus Ukachukwu ke da kamfanin Lingo Nigeria Limited. Ya karbi makudan kudaden talakawan kasar nan daga hannun gwamnati domin aikin gyaran titin, amma ya yi mirsisi bai yi aikin kwangilar da aka ba shi ba.

Kamfanin Lingo na Ukachikwu bai taba yin aikin titin jirgin kasa ko da na daura kwangiri daya tal ba, Amma aka dauki aikin daura kwangirin jirgin kasa har na tsawon kilomita 640 daga Kuru a Jihar Filato zuwa Maiduguri, akan kudi naira bilyan 23.7 aka damka masa.

Ya karbi har naira bilyan 9.4 ya kacalcala wani aiki kamar shacin zanen zamiyar-zakara. Kuma har ya sake neman a kara masa naira bilyan 9.2.

Ya nemi karin kudin tare da rubuta bayan karairayin ayyukan da ya ce ya yi mai yawa. Amma jami’an kula suka gano duk karya ya rubuta, gidoga ce kawai ya tsara.

Gidogar Da Gogarma Ukachukwu Ya Shirya Wa Gwamnari:

A taron da ‘yan kwangila su Ukachukwu suka yi da jami’an gwamnati a ranar 19 Ga Maris, ya yi ikirarin cewa shi ya kammala kusan kashi 60 zuwa 70 na aikin da aka ba shi.

Kuma ya ce har ma jirgin kasa ya fara bi ta wani bangaren layin dogon da kamfanin sa ya daura, ya na daukar daukar mutane daga Kuru zuwa Gombe.

Sai dai kuma rahoton da wakilin mu ya tattaro bayan ya je har wurin, da takardun da wannan jarida ta samu, sun tabbatar da cewa almuri Ukachukwu karya ya ke yi.

Cikin Agusta 2011, Lingo ya karbi naira bilyan 3.5 daga Hukumar Jiragen Kasa. Kuma cikin 2012 an sake ba shi naira bilyan 2.5 daga Asusun SURE-P.

Amma in banda wasu kayan aiki da kamfanin Lingo ya saying ya jibge, har zuwa 2012 din bai yi aikin komai ba.

Wasu jami’an da PREMIUM TIMES ta samu sun shaida mata cewa kamfanin Lingo ya kasa yin komai domin kwata-kwata bai sani ba, kuma bai taba yin aikin titin jiragen kasa ba.

A karshe dai sai da ta kai kamfanin Lingo ya rakito wani kamfanin China matsayin sojan-haya, domin ci gaba da yi masa aikin titin jirgin kasa din.

Kamfanin mai suna CREC5 Co. LImited, ya kai kayan aikin sa cikin 2014.

Ya zuwa 2025 har farkon mulkin Buhari, an biya Lingo tsabar kudi naira bilyan 9.4, kamar yadda takardun biyan kudade da Ukachukwu ya sa hannu a madadin Lingo, a ranar 4 Ga Mayu, 2020 ta tabbatar.

Lingo: Titin Jirgin Kasa Ko Dai Burtalin Shanu?

Ba za a ce kamfanin China da Lingo ya ce dauko haya bai yi aikin komai ba. Ya gi aiki, amma sai dai a kira aikin da ya yi da aika-aika.
PREMIUM TIMES ta ga yadda yadda ya gina titin kwangirin jirgin kasa, na tsaron kilomita 100. Ba tsaye shantal ya shimfida kwaltar ba. Tsilla-tsilla ya yi aikin, kuma marar inganci, ta yadda Lingo ya gina titin jirgin da ko mai keken shanu zai ji tsoron bi a kai. Amma har ya ke neman karin naira bilyan 9 2.

Dukkan zirga-zirgar da PREMIUM TIMES ta yi domin duba-garin titin jirgin, tare da kwararren fannin aikin titin jiragen kasa ta yi.

PREMIUM TIMES ta gano cewa ba a rabu lafiya taakanin ‘yan Chana da Lingo ya dauko haya ba. Domin sun kwashe ya na su ya sa su cikin 2015, sannan suka rubuta wa Ma’aikatar Sufuri wasika a cikin 2017, cewa su na bin kamfanin Lingo bashin naira bilyan 1,551, 898.624. Don haka ma’aikatar ta yi mata zamiyar kudin daga cikin kudin da Lingo ke bin gwamnati ciko.

Har yau dai ba a maida masa amsa ba.

PREMIUM TIMES ta nemi jin wasu bangarorin da ke tankiya, amma ba su bada amsa ba.

Shi kuwa Ukachukwu da aka tambaye shi, sai ya ce ai ba abin kunya ba ne don kamfanin China na bin sa bashin naira bilyan 1.5.

“Ko akwai wanda zai iya yin aikin naira bilyan 23 ba tare da an bi shi bashi ba?

Share.

game da Author