Kungiya ta nemi a bincike zargin Dallara wa Akpabio mari da tsohuwar Darekta ta yi saboda ya nemi cin zarafin ta

0

Wata kungiyar mai zaman kanta dake shirya bukukuwa da kwalliyar mata, ta yi kira ga ministan Neja-Delta, Godswill Akpabio ya gaggauta yin murabus daga mukamin sa na minista.

Kungiyar ta ce bisa ga kalaman tsohuwar shugaban hukumar NDDC, da ta ce ta taba dallara wa minista Akpabio mari da ya nemi ya afka mata don yin lalata da ita, bai kamata ace wai har yanzu yana dare a kujerar minista a Najeriya ba.

” Shima yana daga cikin wadanda ya kamata a tuhuma suna kokarin cin zarafin mata.”

shugaban kungiyar Sarah Anogwi, ta bayyana cewa ganin irin girman wannan zargi, kamata yayi minista Akpabio ya gaggauta yin murabus domin ya wanke kansa.

Yadda Joy Nunieh ta fallasa Akpabio

Tsohuwar shugaban Hukumar Raya yankin Neja-Delta, Joy Nunieh ta bayyana a hira da tayi da talbijin din Arise cewa akwai wata rana da ta sharara wa Ministan Neja Delta mari a gidan holewar sa dake Apo, da ya nemi ya yi lalata da ita.

” Me ya sa bai fadi wa Duniya cewa na sharara masa mari ba a gidan holewar sa dake Apo, Ni ce mace ta farko ‘yar Ogoni da ta taba zabga masa mari, tya fito ya karayata in ya isa.

” Na mare shi ne saboda neman afka mini da yayi, saboda naki amsar cin hancin da ya so ya bani na kudi. bai san cewa ni yar Fatakwal ba ce ba u tsoro kuma kudi baya ruda mu. Tabbas ina tuhumar sa da kokarin afka mani da karfin tsiya.

Idana ba a manta ba, Joy Nunieh, ta zargi Ministan Ma’aikatar Kula da Neja-Delta, Godswill Akpabio da harkallar satar makudan kudade.

Nunieh ta ce a cikin ‘yan watannin da ta yi ta na rikon-kwaryar hukumar, Minista Akpabio a matsayin sa na Ministan Neja-Delta, ya yi ta kokarin tirsasa ta yin rantsuwa a asirce cewa ba za ta fallasa duk wata cuwa-cuwa, harkalla, wuru-wuru, kamaya-maya, lodi da jidar kudaden da aka yi ko za a yi ba.

“Misali, akwai lokacin da ya ce min na shirya takardar bayar da kwangilar bogi ta raba kayan agaji ga al’ummar Neja-Delta da albaliyar ruwa ya yi wa barna.” Inji Nunieh.

Ma’aikatar Neja-Delta da Akpabio ke shugabanci dai ita ce ke kula da ayyukan Hukumar NNDC.

Tsohuwar shugabar ta NNDC, ta shaida wa manema labarai bayan ta fito daga bayyanar da ta yi a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa Mai Binciken NNDC cewa, da ta kuskura ta bi son ran Minista Akpabio ta yi duk abin da ya ke so ta rika yi, to da yanzu ta na can daure a kurkuku.

Ta ce Akpabio ya yi duk wani kokari domin ya tirsasa ta yin rantsuwar ba za ta tona masa asiri ba, amma ta ki.

Tuni wannan bidiyo da Gidan Talbijin na Channels ya nuna, ana ta watsa shi a soshiyal midiya.

Ta ce sau uku Akpabio ya na tirsasa ta domin ta yi rantsuwar ba za ta tona masa asiri ba.

Ta kara da cewa da ta ki yin rantsuwar-,kaffarar,-Akpabio, sai aka rangada fadar shugaban kasa aka gurfana a gaban Sarki Abba, Hadimin Shugaban Kasa a Harkokin Cikin Gida.” Shi ne ya sasanta mu.

Nunieh ta ce tsoro ta ji za ta iya zaman kurkukun shekara biyar cur idan Akpabio ya gina mata rijiya ta rufta.

Ta ce za a iya kama ta a karkashin Dokar Ka’idojin Bayar Da Kwangiloli. Alhali ba ta iya kare kan ta, shi kuma Akpabio ya tsallake rijiya abin sa.

“To sai bayan da na ki amincewa na yi wa Akpabio rantsuwar-kaffara ce sannan ya fara kulla fuggun ganin an cire ni daga kan mukamin.

“Ya ce sai ya xire ni. Daga nan kuma ya fara watsa farfagandar bata min suna da zubar min da kima.” Inji ta.

Kokarin da Premium Times ta yi domin jin ta bakin Kakakin Akpabio, Anietie Ekoong ya ci tura, domin har yau ba a maido amsar tes din da aka tura masa ba.

Takun-saka Tsakanin Akpabio Da Nunieh:

Nunieh ta zama Shugabar Rikon NNDC bayan an cire Akwagaga Enyia cikin Octoba 2019.

Sai dai kuma ita ma din an cire ta watanni hudu bayan nada ta, bayan rika samun bayanan salwantar makudan kudade.

Daga nan ne kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Kemebradikumo Pondei, a madadin ta.

Pondei ne a waccan Alhamis da ta gabata, ya shaida wa Kwamitin Bincike a Majalisar Dattawa cewa, sun kassafa naira bilyan 1.5 a tsakanin su, a matsayin tallafa wa kan su da agajin zaman gida lokacin Coronavirus.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Minista Akpabio ya kitsa algungumancin cire Nunieh daga shugabancin NNDC, aka nada Kemebradikumo.

Mutanen da ke da masaniyar takun-saka tsakanin Akpabio da Nuneih, sun ce mutanen biyu ba su jituwa a tsakanin su.

Yayin da ake tattaunawa da ita, ta ce Akpabio bai taba sa wa takardun ta hannu ba. Sai dai kawai ya hada baki da wasu ‘yan barandan sa su rika shirga karkallar fitar da makudan kudade.

“Ina sane na ki bin sa zuwa Taron Majalisar Zartaswa, domin na rigaya na san irin mummunar gidogar harkallar da ya shirya wa Shugaban Kasa. Na san Dokar Kwangila za ta iya kama ni da laifi, har a daure ni shekaru biyar.”

Nunieh ta ci gaba da bayyana dalla-dallar kwangilolin gidoga da Akoabio ya rika shiryawa. Kuma ta ce duk wasu kudade da za a fitar, sai da sanin sa.

Share.

game da Author