LManoma masu dimbin yawa su na ci gaba da kokawa a kan yadda dokar hana walwala da zirga-zirga da gwamnatin tarayya da jihohi su ka kakaba a lokacin yaki da cutar Coronavirus, cewa ta ja musu dibga babbar asarar kasa fita kasuwanni su sayar da kayan amfanin gonar su. Kuma dokar kullen ta haifar da yankewar abinci.
Wani Mai kiwon kaji a Lagos, mai suna Ayodomun Oluwafemi, ya karyar da farashin kires na kwan kaji daga naira 850 zuwa naira 500. Wannan karyar da farashi ya janyo masa tafka danyar asara fiye da kima.
Ya ce ya karbi asara kiri-kiri domin ya samu kudaden da zai rika ciyar da dandazon kajin da ya ke kiwo, don kada a yi uku babu – wato ba kwai, ba kudi kuma babu kajin.
Amma fa ba duka aka zama daya ba. Akwai masu hamdala da murnar cewa kakar bana ta yi musu kyau sun samu alheri da kuma dama ce suka samu domin komawa gona.
Irin su Itoro Emmanuel ya ce shi maimakon ya shiga kunci lokacin da aka kulle jama’a cikin gida, sai ma ya samu alheri da riba mai tarin yawan gaske.
“Yayin da jama’a da dama suka shiga kunci a lokacin da aka kulle mutane a gida, ni kuwa sai na yi amfani da wannan dama na rika yini a gona. Amma kafin wannan lokacin, sai dai na leka kawai na koma gida.” Inji Emmanuel, mai gona kusa da Jami’ar Uyo.
Ire-iren kananan manoma masu noma abincin ciyar da iyali da kuma samun na kudin cefane, sun ce a lokacin dokar kulle sun maida hankalin su kacokan a kan gonakin su. Wadanda suka kasance gidajen su babu nisa zuwa gonar su, a kasa su kan taka daga gida zuwa gona.
Kulle mutane da aka yi a gida tun daga ranar 30 Ga Maris, ya durkusar da tattalin arzikin kasa sosai. Ganin yadda dokar ta yi illa, sai gwamnati ta bari ana ci gaba da safarar kayan abinci a manyan wurare har ma da irin su takin zamani.
Ganin yadda Coronavirus ta yi raga-raga da tattalin arzikin Najeriya, sai masana suka bada shawarar cewa harkar noma ce kadai za ta iya tsamo tattalin arzikin kasar nan daga ramin da ta fada gaba dubu.
Wata mata mai suna Aaron, wadda ma’aikaciyar da ta yi ritaya ce, kuma mai ‘ya’ya shida, ta fara noma da gona guda daya.
Amma yanzu ta yi karfin noma ganyen miya, kokumba, yalo da doya.
Ta ce na na samun ribar akalla naira 300,000 a noman da ta ke yi. Sannan kuma a ciki su ke dibar abincin da suke ci.
A jihar Akwa Ibom bincike ya nuna cewa lokacin dokar zaman gida dole, manoma maza da mata har ma da kananan yara, sun maida hankali kacokan kan zuwa gona.
Christiana Johnson ta ce ta ji ta yi farin ciki da aka yi dokar hana zirga-zirga a lokacin fara yin dashe da shukar amfanin gona.
“Tunda ni mace ce mai bin doka da oda, sai na yi amfani da bin umarnin wannan doka, na yi zama na a gida, ba ni fita, sai noma na ke yi a bayan gida na.
“Da babu wannan dokar ai ban ga yadda za a yi na zauna har na yi noma a bayan gida na ba.”
Masana dai sun ci gaba da cewa bunkasa harkar noman wata kafa ce fadada samun kudaden shiga a lokacin da farashin danyen man fetur ya fadi kasa warwas, sannan kuma hanya ce mikakkiya ta bunkasa wadatar abinci a cikin kasa.