Yadda Buhari da kwamitin Zartaswar APC suka karya dokar jam’iyyar, suka nada gwamnoni cikin Kwamitin Riko

0

Nadin da aka yi wa wasu Gwamnonin Jam’iyyar APC cikin Kwamitin Shugabannin Riko, ya karya dokar jam’iyyar APC, kamar yadda PREMIUM TIMES ta bincika kuma ta bayyana.

A ranar Alhamis ne Babban Kwamitin NEC na zartaswa na APC ya rushe kwamitin Gudanarwa na NWC tare da nada mambobin kwamitin riko su 13, cikin su kuwa har da gwamnoni uku.

An dora musu nauyin rikon ragamar jam’iyyar har tsawon watanni shida nan gaba.

A taron da uwar jam’iyyar ta yi a Fadar Shugaban Kasa, an dora wa sabbin Shugabannin Riko su tabbatar sun shirya taron gangamin jam’iyya a cikin wadannan watanni shida, domin a zabi cikakkun shugabannin jam’iyya.

An kuma umarci mambobin APC kowa ya janye duk wata kara da korafe-korafen da aka kai juna a kotu.

Sun kuma amince da zaben da aka yi wa Osagie Ize-Iyamu a matsayin dan takarar APC a zaben jihar Edo, wanda za a yi a ranar 19 Ga Satumba.

Cikin wadanda suka halarci taron har Buhari, Mataimakin sa Yemi Osinbajo da kuma gwamnonin APC na kasar nan.

Gwamnoni uku da aka nada cikin shugabancin kwamitin su na Yobe, Mai-Mala Buni, wanda kuma shi aka nada Shugaban Riko na Kasa, sai Isiaka Oyetola na Osun da kuma Sani Bello na Neja.

Antoni Janar kuma Ministan Harkokin Shari’a na Kasa, Abubakar Malami ne ya rantsar da Gwamna Buni a matsayin Shugaban Riko.

Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta binciko cewa Kwamitin Zartaswar APC ya karya Sashen Dokar APC na 17 (v) na 2014 da aka yi wa kwaskwarima a cikin shekarar 2014 din.

Ga Abin Da Dokar Ta Ce:

“APC ba ta yarda kuma ba ta amince mutum ya kasance ya na rike da mukamin shugabanci a jam’iyya, kuma ya na rike da mukami a cikin gwamnati ba.”

Wannan sashe na doka kenan ya haramta gwamnonin uku zama shugabannin rikon jam’iyyar APC kenan.

Wani lauya mai suna Ken Asogwa, ya bayyana rashin jin dadin yadda APC ta karya dokar da ta gindaya da kan ta, duk kuwa da cewa a baya Kotun Koli ta gargadi jam’iyyun siyasa su daina karya dokokin da suka rattaba a cikin jam’iyyun su, domin rage yawan kararraki a gaba.

Sauran masana da lauyo yin da suka zanta da PREMIUM TIMES, duk sun nuna mamakin irin yadda APC ta tafka wannan gagarimin kuskuren da ake ganin zai rike mata wuya a gaba, har ta yi da-na-sani.

Tuni dai har bangaren NWC da aka tsige aka nada wasu, sun yi barazanar garzayawa kotu.

Masu hangen nesa na ganin cewa duk wani zabe da APC za ta shiga a karkashin wadannan Shugabannin Riko, zai zama haramtacce kenan.

Wato ko da ta yi nasara a zabukan gwamnan Edo da Ondo, kotu za ta iya kwacewa ta bai wa jam’iyyar da ta yi ta biyu.

Share.

game da Author