Bidiyon da aka nuno wasu na lalata cikin motar Majalisar Dinkin Duniya abin takaici ne -Shugaban UN

0

Majalisar Dinkin Duniya ta fara bincike da farautar yadda aka yi har wasu suka yi lalata a cikin motar Majalisar, mai dauke da tambarin “UN”.

Kakakin Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Stephane Dujarric ce ta sanar da fara binciken tare da cewa abin takaici ne da tir kuma abin kwatagwalci ga UN.

Wani bidiyo da aka rika watsawa ya nuno ana lalata a cikin motor mai tatoyi hudu, a lokacin da motar ke gudu.

Motar fara ce, mai tambarin UN, wato Majalisar Dinkin Duniya, da aka hakkake ta na aiki ne a Sasanta Bangarori a Isra’ila.

Kafafen Yada Labarai sun hakkake cewa wani namiji ne aka nuno ya na lalata da wata mace mai sanye da jajayen kaya, kuma ita ce ke zaune a kan cinyar namijin.

Sannan kuma akwai direba da kuma wani fasinja mai aske da kan sa babu gashi da ke zaune a gaban mota, gefen direba.

An tabbatar da cewa an dauki bidiyon ne a kan titin Ha Yarkon da ke cikin birnin Tel Aviv, Babban Birnin Isra’ila.

Amma dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce ba ta tabbatar da inda aka dauki bidiyon lalatar ba tukunna.

“Majalisar Dinkin Duniya ta firgita matuka da aka nuno ana lalata a cikin motar UN. Wannan abu ne da ba za a bari ya wuce haka ba tare da daukar kakkausan hukunci ba.

“Kuma abu ne da ya kauce wa dokoki da ka’idojin da UN ke aiki a kan su day wadanda ta gindaya wa ma’aikatan ta.

“Mu na sane da bidiyon tun kwanaki biyu da suka gabata. Kuma tun daga lokacin mu ka fara bincike a kai.

“Bincike ya yi nisa kuma tuni mun gano daidai wurin da aka yi lalatar. Sannan su ma malalatan mu na kusa da tantance ko su wane ne.

Idan ba a manta ba, cikin 2019 UN ta karbi rahotannin yadda jami’an ta suka rika yin lalata da mata ba da son ran matan ba har sau 174.

A cikin korafe-korafen 175, an tababtar da 16, an kasa tabbatar da 15, sauran kuma har yanzu ana ci gaba da bincike.

Share.

game da Author