Wasu ‘yan bindiga sun kashe Hakimin ‘Yantumaki, cikin Karamar Hukumar Danmusa a Jihar Katsina.
Sun kashe Abubakar Atiku awanni kadan bayan wasu ‘yan bindiga sun yi wa Shugaban APC na Karamar Hukumar Batsari takakkiya har gida suka yi masa kisan gilla.
Lamarin ya faru da dare ranar Lahadi, inda maharan su ka shafe awa biyu a ‘Yantumaki su na fakon hakimin, wanda suka bindige yayin da ake ruwan sama, wajen 12 na dare.
Majiya ta tabbatar da cewa an harbi dogari daya ya ji ciwo. Said dai kuma an ce harsashe ne ya wuce ya same shi, ba shi aka yi saiti ba.
‘Yan bindigar dai ba su kashe kowa ba banda hakimin. Kuma suka yi tafiyar su.
Kisan hakimin ‘Yantumaki ya faru a ranar da aka bindige Shugaban APC na Karamar Hukumar Batsari, duk a cikin Jihar Katsina.
Shugaban mai suna Abdulhamid Sani, ‘yan bindiga sun yi masa kisan-gilla ne yayin da ya je kauyen su Dumburawa da niyyar sasanta batun rabon gado.
Majiya da kuma Tsaskar Labarai a Katsina sun tabbatar cewa Abdulhamid Sani ya na daga cikin masu sasantawa da ‘yan bindiga a Karamar Hukumar Batsari.
“To wani dan bindiga mai suna Kwalli ya shiga gari, sai ‘yan banga suka kama shi, suka mika shi ga ‘yan sanda.
“Sai shuganan gungun su Kwalli mai suna Manu Wargaje, ya kira Abdulhamid ya ce ya na so ya sa baki a saki Kwalli.
“Abdulhamid ya ce ba zai iya ba, domin magana ta kai ga ‘yan sanda.
“To su dama su Manu da Kwalli ba su cikin gungun ‘yan bindigar da suka tuba.
“Sai suka samu wani magulmaci (infoma), suka ba shi kudi, suka ce duk ranar da Shugaban APC ya je kauyen su, ya sanar da su.
“Ranar da ya je Dumburawa batun rabon gado, sai ga Manu Wargaje shi da wasu mahara biyu a kan babura biyu. Suka samu Abdulhamid su ka ce za su tafi da shi, sai an sakar musu Kwalli, sannan su sake shi.
“Abdulhamid ya ce ba zai bi su ba. Jama’a kuwa suka kewaye su, aka yi cirko-cirko. Ganin haka, sai Manu ya dirka masa bindiga, amma ta ki tashi.
“Da su ka ga haka, sai suka kama shi, su na duka da sanda, kuma suka bankare hannayen sa, suka harbe shi a kasan hamatar sa. Nan ya fadi, daga baya ya rasu.”
Wata majiya ta tabbatar da cewa Fulanin da suka tuba, sun bi su Manu Wargaje sun kashe a cikin daji. Kuma suka kira jama’a domin a je a dauki gawarwakin su, kuma a shaida.
Kakakin Yada Labaran ‘Yan Sanda na Katsina ya tabbatar da kisan Hakimi da na Shugaban APC.
Idan ba a manta ba, shekarun baya mahara sun yi wa Dagacin Birchi takakkiya har gida cikin Karamar Hukumar Kurfi, suka kashe shi.
Discussion about this post