Zagin Musulmi fasiƙanci ne, cin mutunci, ɓatanci, tozarta Musulmi haramun ne, zagi da cin mutuncin wanda ba Musulmi ba haramun ne da Nassin Al-Qur’ani.
Wannan na Musulmi ke nan da wanda ba Musulmi ba. Na shugaba yafi muni saboda Allah Ya shigar da ɗa’ar shugabanni (musamman shugabanni Musulmai) cikin ɗa’arSa. Saboda haka ba ƙaramin haɗari ba ne zagi ko cin mutuncin shugaba a kowane mataki a cikin Al-Ummah, matuƙar yana ɗaukan ma’anar shugaba.
Mu kiyaye! Domin duk wanda Allah Ya tuhume shi me yasa ka yi kaza ya halaka saboda ba shi da mafita.
Saboda me zaka riƙa zagin mutane, musamman shugaba alhali yin hakan ya saɓa ma koyarwar Musulunci? Duk abin da ya saɓa ma koyarwar Shari’ah, to, babu ko shakka ƙofar halaka ce.
Ɗaya daga cikin magabata na ƙwarai yana cewa: “Mutane ba za su riƙa aibanta shugabansu ba face Allah Ya haramta musu alkhairansa” galibin masu cin mutuncin shugabanni masu da’awar ƴancin Dimokaraɗiya ne ko wanɗada suka tasirantu da ɗabi’unsu, wanda wannan ƴancin kishiyar na Musulunci ne, hasalima Dimoraɗiya addini ce mai zaman kanta. Duk wanda aka tashe shi Gobe Qiyamah akan addinin Dimokaraɗiya ya halaka.
Dimokaraɗiya yaudara ce tsantsa kuma babu abin da take kawowa sai raba kan mutane da tabbatar da rashin haɗin kansu da dangogi kala-kala na ɓarna da sharri. Duk abin da zai raba kan mutane, ya hana su haɗin kai domin neman abin duniya, to, sharri ne shi a karan kansa da halaka.
Ke nan mulkin soja yafi Dimokaraɗiya alheri agaremu saboda yana hana mu cin mutunci da zagin mutane da muguwar Addu’a ga mahukunta saboda tsoron fushin hukuma tunda mun kasa gane Dimokaraɗiyar ba ƴancin cin mutunci da tozarta mutane ba ne.
Babu abin dake saurin kai mutane Al-Jannah kamar halaye da ɗabi’u na kirki da kyakykyawar mu’amala, haka zalika babu abin dake saurin kai mutane wuta kamar muyagun halaye da mummunar mu’amala da yau sun yi katutu a cikinmu. Dole sai mun gyara tarbiyarmu idan muna son dacewar Lahira. Allah Ya ƙara shiryar damu hanyarSA Madaidaiciya, ameen.