Sama da mutum 500 cikin mutum 979 da suka rasu a Kano duk Korona ce sanadi

0

Ministan Kiwon Lafiya Enahire Osagie ya bayyana cewa sakamakon binciken da aka yi sun nuna cewa mutum 400 zuwa 587 cikin mutum 979 da suka mutu a Kano an gano cewa cutar Korona ce sanadi.

Enahire ya bayyana haka a jawabin mako-mako kan ayyukan korona da kwamitin shugaban kasa keyi a Najeriya

Idan ba a manta ba, jihar Kano ta yi fama da mace-macen mutane da dama, Malaman Jami’a, Sarakuna, manyan mutane da ‘yan jihar sun yi ta rasuwa a cikin watannin da suka wuce.

Sai dai sakamakon binciken da aka yi na farko ya nuna cewa da yawa sun rasu ne a dalilin fama da suka yi da zazzabin cizon sauro da Sankarau.

Amma kuma Sani Gwarzo, Kodinaton Kwamitin dakile yaduwar Coronavirus, na jihar Kano ya bayyana wa Cable cewa cutar Coronavirus ne ya kashe mutane a Kano.

” Saboda haka idan mutane zasu farka daga barcin da suke yi su farka domin nan da sati daya ko kwanaki sakamakon binciken zai fito kowa zai gani wa kansa.

Yanzu da aka samu sakamakon binciken da aka yi, mafi yawan wadanda suka mutu duk Korona ce ta kashe su sannan mafiyawan su sun zarce shekaru 65.

An samu rahoton irin wannan mace-mace a jihohin Jigawa, da Bauchi da akalla mutum 150 suka rasu cikin dan kankanin lokaci.

Share.

game da Author