Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 315 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Litini.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini, sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum 128, FCT – 34, Rivers – 32, Edo – 28, Oyo – 22, Kaduna – 20, Gombe – 13, Ogun – 8, Plateau – 5, Delta – 7, Kwara – 7, Kano – 5, Bauchi – 4, Katsina – 2.
Yanzu mutum 12,801 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 4040 sun warke, 361 sun rasu.
Duk da yawan mutane da ake samu sun kamu da cutar a kullum a Najeriya, wasu da dama na ganin har yanzu ba a yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 5, 895 cases, sai Jihar Kano – 1,004, FCT – 986, Edo – 429, Katsina – 397, Oyo – 387, Rivers – 364,Kaduna – 363, Ogun – 363, Borno – 356, Bauchi – 295, Jigawa – 283, Gombe – 230, Delta – 155, Kwara – 142, Sokoto – 129, Plateau – 120, Nasarawa – 112, Ebonyi – 103, Abia – 83, Zamfara – 76, Imo – 68 Yobe – 52, Osun 49, Akwa Ibom – 45, Niger – 44, Adamawa – 42, Ondo – 42, Kebbi – 35, Enugu – 30, Bayelsa – 30, Anambra – 29, Ekiti – 29, Taraba – 18, Benue – 13, and Kogi – 3.
Discussion about this post