Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Wadume gogarman garkuwa da mutane da mutum 6 a kotu

0

A ranar Litinin din nan ce Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da gogarman masu garkuwa da mutane a jihar Taraba mai suna Bala Hamisu a gaban kotu.

An gurfanar da Hamisu wanda aka di sani da sunaWadume tare da wasu mutane shida, bayan sun shafe watanni goma cur a tsare.

An kama Wadume a Kano, bayan da ya tsere daga hannun ‘yan sanda, lokacin da sojoji suka bude musu wuta a wani gari mai suna Gidan Waya a jihar Taraba, cikin watan Agusta, 2019.

A Litinin din Nan bayan Mai gabatar da kara Shuaibu Labaran ya yi wa Mai Shari’a Nyako bayani, ya ce mutanen da ake zargin su 16 ne, amma bakwai kadai suka kama.

Dalilin Haka ne aka rage tuhumar da ake yi musu,daga 16 zuwa 13. Don haka sai ya nemi Mai Shari’a da ya same ranar da za a fara sauraren kara ka’in da na’in.

Wadanda aka gabatar din sun hada da Hamisu Bala (Wadume), Aliyu Dadje, Sufeto Umar Bala, Uba Bala, Bashir Waziri, Zubairu Abdullahi da kuma Rayyan Abdul.

Dukkan su bakwai din dai sun shaida wa kotu cewa ba su aikata laifin yin garkuwa, karbar naira milyan 106 kudin fansa, mallakar bindigogi 6 samfurin AK 47 ba tare da lasisin amincewa ba, da sauran su.

Sai dai kuma Sufeton ‘Yan Sanda na Kasa da Ministan Shari’a sun karbi gabatar da Shari’a har an yi masu karin tuhumar su da laifin fashi da kisa.

Kotu ta aza ranar 22 Ga Yuni za a fara sauraren shari’ar gadan-gadan.

WAIWAYE: Yadda Wadume Ya Tsere Kafin A Sake Kama Shi A Kano

An buga wannan bayani da ke Kasa tun a ranar 15 Ga Agusta, 2019.

DALLA-DALLA: Yadda gogarman masu garkuwa da mutane, Wadume ya tsere a kwale-kwale.

Wannan wani sabon binciken kwakwaf ne da PREMIUM TIMES ta gudanar, inda ta bankado harkalla, kulle-kulle da kisan-fin-karfin da sojoji suka yi wa zaratan ‘yan sanda uku, sannan suka kubutar da gogarman mai garkuwa da mutane daga hannun ‘yan sanda. Dama Hausawa na cewa “makashin ka na gindin ka.” Ku karanta ku ji yadda wannan jarida ta baje muku komai a kan faifai.

An yi wa wadannan zaratan ‘yan sanda masu zakulo masu garkuwa da mutane su uku kisan-gilla ne a daidai kauyen Gidinwaya, wanda ke tsakanin garin Ibi da Wukari a Kudancin Jihar Taraba.

Akwai shingen sojoji a kan kwalta, daidai Gidinwaya, kuma sojojin da ke tsaro da binciken motoci masu wucewa a Gidinwaya din ne suka bude musu wuta. Sojojin daga Bataliya ta 93 da ke Takum ne aka tura su domin aiki a shingen na kan kwalta.

Wannan kisan-gilla ya haifar da babbar barazana ga lamarin tsaron kasar nan tare kuma da haifar da rashin jituwa mai tsami tsakanin Sojojin Najeriya da ‘yan sandan Najeriya.

Jami’an ‘yan sandan da aka bude wa wuta sun a tafiya ne a cikin wata fatar mota bas, sun fito ne daga Ibi, inda suka kamo wani rikakken mai garkuwa da mutane mai suna Hamisu Bala, wanda aka fi sani da Wadume.

Rahoton Wakilin PREMIUM TIMES daga wurin da aka yi kisan

Wakilin PREMIUM TIMES ya ziyarci har wurin da sojoji suka kashe ‘yan sandan a Gidinwaya da ke kan titin Ibi zuwa Wukari.

Binciken da ya yi a can da za ku karanta a yanzu, har da ikirarin da mutanen kauyen suka yi, wadanda ya tattauna da su dangane da yadda abin ya faru.

Binciken PREMIUM TIMES a kauyen ya sha bamban da abin da sojohi suka bayyana cewa ya faru a kauyen na Gidinwaya.

A halin da ake ciki a yanzu, kauyen Gidinwaya kewaye ya ke da sojoji, wasu a kwak-kwance cikin shirin damarar yaki a cikin daji, tsallaken inda aka bindige ‘yan sandan. Sun sa-ido sosai su na lura da yadda mazauna kauyen ke gudanar da harkokin su.

Mutanen kauyen su kuma su na cikin tsaro da fargabar abin da zai iya samun su idan suka fai gaskiyar abin da ya faru dangane da kisan Sufeto Mark Ediale, Sajen Usman Danzumi da Sajen Dahiru Musa. Sai kuma wani farar hula mai suna Jibrin da shi ma a lokacin sojojin suka harbe su tare.

SOJOJI KO ‘YAN SANDA: Wa ya fara buɗe wuta

A sanarwar da Kakakin Yada Labarai na Sojojin Najeriya, Sagir Musa ya fitar ranar Larabar makon jiya, ya bayyana cewa sojoji sun yi tsammanin masu garkuwa da mutane ne. Kuma an tsayar da su, amma suka ki tsayawa. Sannan kuma Sagir ya ce ‘yan sandan ne suka fara bude wa sojojin wuta.

Wasu shaidu guda biyu sun tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan sandan ba su bude wa sojoji wuta ba, kamar yadda su mahukuntan sojojin suka yi ikirari.

Amma kuma shaidun sun tabbatar wa wakilin PREMIUM TIMES cewa ‘yan sandan ba su tsaya a shingen sojojin ba.

An bindige ‘yan sandan kamar mita 100 daga inda shingen sojojin ya ke.

Yadda yaran Wadume Suka riƙa bin Ƴan sanda a baya tun daga Ibi

“Wato su yaran Wadume sun rika bin motar da ‘yan sanda suke ciki dauke da ogan su tun daga Ibi, bayan da suka kamo shi daure da ankwa.” Haka wata kwakkwarar majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES, kuma majiyar ta ce a kan idon ta al’amarin da ya faru a Gidinwaya ya faru.

“Su yaran Wadume ne suka shaida wa sojojin da ke shingen bincike a nan Gidinwaya cewa farar mota bas da ke a gaban su, masu garkuwa da mutane ne suka sato Alhaji Hamisu Wadume. Dama kuma shi Hamisu Wadume din sojoji duk sun san shi farin sani, za su iya yin komai domin su kare lafiya ko ran sa.”

Majiyar ta ce daga nan ne sai sojojin suka shaida wa abokan aikin su da ke shingen kan hanya da ke daidai Gidinwaya cewa wato shinge na biyu, wadanda su din ne suka bi su, suka bindige su.

Majiyar PREMIUM TIMES ta shaida wa wakilinmu cewa farar hular da aka kashe mai suna Jibrin, wani magini ne, kuma ya ma san shi sosai. Ya ci gaba da yi wa wakilin mu karin bayanin cewa Jibrin ya na kwarmata wa ‘yan sanda masu kamo ‘yan garkuwa duk wani sirrin yadda za a kamo su.

Share.

game da Author