Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 416 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Litini.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Litini, sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 192, Edo – 41, Rivers – 33, Kaduna – 30, Kwara – 23, Nasarawa – 18, Borno – 17, FCT – 14, Oyo – 10, Katsina – 7, Abia – 5, Delta – 5, Adamawa – 4, Kano – 4, Imo – 3, Ondo – 3, Benue – 2, Bauchi – 2, Ogun 2 and Niger – 1.
Yanzu mutum 10,500 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 3, 122 sun warke, 299 sun mutu.
Duk da yawan mutane da ake samu sun kamu da cutar a kullum a Najeriya, wasu da dama na ganin har yanzu ba a yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata ba a kasar.
Wasu kuma har yanzu suna ganin ba babu ma cutar a kasar.
Jihar Legas na ci gaba da samun daruruwan mutanen da suka kamu da cutar Korona babu kakkautawa.
A ranar Litinin kawai, jihar Legas ta samu karin mutum 192. Akalla jihohi 20 sun samu karin mutanen da suka kamu da kwayoyin cutar Korona ranar litini.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 5, 135, sai jihar Kano – 958, FCT – 674, Katsina – 371, Edo – 325, Oyo – 302, Kaduna – 288, Borno – 288, Ogun – 280, Jigawa – 270,, Bauchi – 240, Rivers – 239, Gombe – 161, Sokoto – 116, Kwara – 111, Plateau – 105, Delta – 88,, Nasarawa – 80, Zamfara – 76, Yobe – 52, Akwa Ibom – 45, Osun – 45, Adamawa – 42, Ebonyi – 40, Imo – 39, Niger – 33, Kebbi – 33, Ondo – 28, Bayelsa – 21, Ekiti – 20, Enugu – 18 Taraba – 18, Abia–15, Anambra – 1, Benue – 9 da Kogi – 2.
Discussion about this post