Kodinatan kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar cutar Covid-19 Sani Aliyu ya bayyan yadda tsarin babi na biyu na sassauta dokar hana walwala a kasar nan zai gudana.
Aliyu ya ce sassauta dokar da wadannan sabbin tsare-tsare zasu fara aiki ne daga ranar 2 zuwa 29 ga watan Yuni.
Idan ba a manta ba a ranar 27 ga watan Afrilu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya janye dokar zaman gida dole a Abuja, Legas da Ogun da yayi aiki na tsawon makonni biyar.
Yanzu dokar hana walwala zai fara aiki ne daga karfe 10 na dare zuwa 4 na asuba.
A ranar Litini ne shugaban kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar cutar Covid-19 kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya Sanar cewa tsarin babi na biyu na sassauta dokar hana walwala zai fara aiki ranar Talata biyu ga watan Yuni.
Ga yadda sabbin dokokin suke
Dokar hana walwala
Daga yanzu za a rika gudanar da harkoki da walwala daga karfe 4 na asuba zuwa 10 na dare.
Bankuna
Gwamnati ta ce duk bankunan dake kasar na za su dawo aiki kamar yadda suke a da.
Ma’aikatan banki za su rika zuwa aiki daga karfe 8 na safe zuwa 2 na rana daga ranar Litini zuwa Juma’a.
Bude wuraren ibada
Gwamnati ta ce gwamnatocin jihohi ne za su tsara yadda za su saki mutane da tsara yadda za su rika zuwa wuraren ibada. Sai dai ta kara da cewa dokar yin nesa nesa da juna da kuma yin amfani da man tsaftace hannu da wanke hannu na daga cikin sharuddan da dole mutane su bi.
Dokar hana tafiye-tafiye
Gwamnati ta ce har yanzu dokar hana tafiye-tafiye na nan daram daga jiha zuwa wata jihar. Banda jigilar kayan abinci da magunguna
Ofisoshi
Ma’aikatan gwamnati za su koma aiki.
Zirga-zirgar Jiragen sama
Daga ranar 21 ga watan Juni jiragen sama za su fara zirga-zirga a fadin Kasar nan.
Gwamnati zata gana da masu mallakin Kamfanin jiragen sama na kasa domin tsara yadda za a dawo da zirga-zirgar tare da kiyaye sharuddan kauce wa kamuwa da yada annobar Korona.
Makarantu, Otel da gidajen cin abinci
Gwamnati ta ce otel a kasar nan za su iya ci gaba da aiki.