Tsohon Gwamnan Imo, kuma Sanata a yanzu, Rochas Okorocha, ya bayyana cewa ba ya goyon a hana almajirci.
Okorocha ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi cikin harshen Hausa da BBC HAUSA.
Ya ce almajirci ba abin kyama ba ne, domin ya samo asali ne daga hijirar da Annabi Muhammadu (SAW) ya yi daga Makka zuwa Madina.
“Almuhajir shi ne almajirci. Kuma idan ka tuna, sun fara tun daga lokacin da Annabi Muhammad (SAW) ya taso daga Makka zuwa Madina.”
Rochas ya ce magana ita ce a hada hannu a tara abin da za a inganta karatun yaran, ba wai a kora su zuwa garuruwan su ba.
Ya ce kamata ya yi a koya musu noma da sauran sana’o’in da za su iya. A kuma inganta ilmin su.
“Wadanda Allah ya ba abin hannu su bada gudummawa wajen bunkasa tsarin karatun almajirai. Saboda ko an maida su gidajen su, ba a magance matsalar ba.
“Yaran nan fa ba laifin su ba ne. Haihuwar su aka yi, suka tashi suka tsinci kan su a gidan wadanda ba su da hali.” Inji Okorocha.
Ya tunatar da irin gudummawar inganta yara wajen ilmantar da su da ya ce Gidauniyar Rochas Foundation ke yi a Arewa.
“Yanzu haka ina da makaranta a Sokoto, Zaria, Bauchi, Yola, Kano da wasu garuruwa.”
Ya ce akwai matsaloli a Arewa, wadanda ya ce hana almajirci ba maganin su zai yi ba, sai ma kara wasu dimbin matsalolin.