Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 587 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Talata.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum Legas 155, Edo – 75, FCT – 67, Rivers – 65, Oyo – 56, Delta – 50, Bayelsa – 25, Plateau – 18, Kaduna – 18, Enugu – 17, Borno – 12, Ogun – 12, Ondo – 7, Kwara – 4, Kano – 2, Gombe – 2, Sokoto – 1 da Kebbi 1
Yanzu mutum 17735 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 5967 sun warke, 469 sun rasu.
Duk da yawan mutane da ake samu sun kamu da cutar a kullum a Najeriya, wasu da dama na ganin har yanzu ba a yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum,7,616, Sai FCT – 1,391, Kano – 1,160 Rivers – 696 Edo – 695, Oyo – 661, Ogun – 586, Kaduna – 490, Borno – 457 Gombe – 443, Bauchi – 430, Katsina – 414, Delta – 367, Jigawa – 317, Plateau – 186, Nasarawa – 177, Abia – 173, Kwara – 172, Ebonyi – 162, Imo – 159, Sokoto – 133, Bayelsa – 111, Enugu – 93, Ondo – 89, Zamfara – 76, Kebbi – 67, Anambra – 66, Niger – 66, Yobe – 55, Osun – 50, Akwa Ibom – 48, Adamawa – 42, Benue – 36, Ekiti – 30, Taraba – 18, Taraba – 18, and Kogi – 3.