Dakataccen Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa ya karbi kaddarar hukumcin Babbar Kotun Daukaka Kasa ta Tarayya, wadda ta jaddada dakatarwar da Babbar Kotun Abuja ta yi masa.
Da ake tattaunawa da shi a Gidan Talbijin na Channels, Oshiomhole ya ce amince da hukuncin kotu, kuma tuni ya janye daga kan kujerar shugabancin Jam’iyyar APC, har an nada na riko.
Ya ce shi mutum ne mai bin umarnin kotu. Don haka ya rungumi kaddara, amma kuma zai tuntubi lauyoyin sa, domin su ba shi shawarar mataki na gaba da zai dauka.
Mataki daya tal ne dai ya rage wa Oshiomhole, shi ne na garzayawa Kotun Koli.
Kotu ta jaddada dakatar da shi a daidai lokacin da APC ke cikin ruguguwar rudanin zaben gwamnan jihar Edo, jihar da Oshiomhole ya fito, inda kuma ya yi gwamna tsawon shekaru takwas.
Tun bayan da ya zama shugaban APC ya ke ta janyo wa jam’iyyar rigingimun da suka haifar mata asarar jihohi da dama. Daga ciki akwai jihohin Zamfara, Bayelsa da Ribas.
OSHIOMHOLE: Ya Aka Yi Ya Haihu A Ragaya?
Babbar Kotun Abuja ta dakatar da Oshiomhole ne tun a cikin watan Maris, bayan da wani lauya mai suna Oluwole Adolabi ya kai korafi a kotu.
Afolabi ya rubuta wa kotu korafin a madadin wani jigon jam’iyyar APC da ke mamba na Kwamitin Zartaswa.
Ya shigar da korafin cewa haramun ne Oshiomhole ya ci gaba da shuhabancin APC na kasa, tunda Jam’iyyar APC Reshen Mazabar sa da ke Etsako, Mazaba ta 10, ta dakatar da shi tunda daga tushen asalin kauyen su a jihar Edo.
An dakatar da Oshiomhole ne sanadiyyar rikicin da ya ara ya yafa, ya ke yi tsakanin sa da Gwamna Obaseki na jihar Edo.
Tun a cikin watan Janairu aka shigar da karar, amma sai Maris aka yanke hukunci.
Oshiomhole ya garzaya Babbar Kotun Daukaka Kara, wadda ta dakatar da dakatarwar da aka yi wa Oshiomhole, zuwa ranar da ta ce za ta yanke hukunci.
A hukuncin da Babbar Kotun Daukaka Kara ta Yanke a ranar Talata, ta jaddada cewa dakatarwar da Babbar Kotun Abuja ta yi masa, daidai ne, don haka ya dakatu.
Sannan kotu ta umarci ya gaggauta sauka, a nada Shugaban Riko kamar yadda dokar jam’iyyar ta tanadar.
Discussion about this post