Shugaban kwamitin yaki da cutar Covid-19 na jihar Imo Maurice Iwu ya bayyana cewa gwamnati ta rufe majalisar dokokin jihar na tsawon makonni biyu.
Iwu ya ce gwamnati ta yi haka ne bayan daya daga cikin ‘yan majalisan ya kamu da cutar Covid-19.
Ya ce za kuma a yi wa haraba da zauren majalisar feshin magani domin kashe kwayoyin cuta yayin da majalisar ke rufe.
Iwu ya ce dan majalisar da ya kamu da cutar na killace a gida tare da matarsa.
Sannan sauran ‘yan majalisar guda 26 tare da masu taimaka musu sun bada jinin su domin a yi musu gwajin cutar.
Bayan haka Iwu ya ce wata mata dake dauke da cutar ta rasu bayan ta haifi tagwaye a jihar.
Ya ce hakan ya kawo adadin yawan mutanen da suka mutu a jihar zuwa biyu.
Iwu ya ce ma’aikatar kiwon lafiya na gudanar da bincike domin gano wadanda za su iya kamuwa da cutar a dalilin cudanya da wadanda suke dauke da cutar.
Ma’aikatan sun gano mutum 135 da suka kamu.
Yanzu haka mutum 92 na kwance a asibiti kuma an sallami mutum 43 daga cikin su.
Gwamnati ta yi kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar domin samun kariya daga cutar.