Buhari ya kafa tarihin gudanar da taron jam’iyya a zauren Majalisar Fadar Shugaban Kasa

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa tarihin zama shugaba na farko da ya shirya taron siyasa a Zauren Taron Fadar Shugaban Kasa, a Abuja.

A ranar Alhamis ce Buhari ya shirya taron na Majalisar Zartaswar APC, zauren da gwamnatin Najeriya ta kebe musamman saboda tarukan da suka jibinci sha’anin mulki da gudanarwar gwamnati.

Tsohon Shugaban Mulkin Soja Ibrahim Babangida ne ya gina zauren Majalisar cikin shekarun 1990, a Fadar Gwamnatin Tarayya da ke kira Aso Rock.

A cikin wannan katafariyar majalisa ce shugabannin da suka gabata, suka rika shirts taruka da ministoci da kuma Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa da Majalisar Kolin Tsaro ta Kasa.

Dukkan wadannan taruka duk sha’anin mulki ne da gudanarwar al’amuran gwamnati ake shiryawa, ba taron siyasa ba.

Kuma a ciki ne wasu shugabannin ke karbar bakuncin masu kawo musu ziyara.

Duk da cewa babu wata dokar da ta hana gudanar da taron siyasa a cikin Zauren Fadar Shugaban Kasa, wannan dai ne karo na farko da aka taba shirya irin wannan taron, tun cikin shekaru 30 da gina majalisar.

Wannan ne kuma karo na farko da shirya irin wannan taron siyasa tun bayan dawowar mulkin dimokradiyya a cikin 1999.

A lokacin mulkin PDP, tun daga kan Olusegun Obasanjo har zuwa Umaru Yar’Adua da Goodluck Jonathan, a hedikawatar PDP suke gudanar da irin wannan taron.

Ita ma APC din tun bayan hawa mulkin Buhari a 2015, a hedikwatar jam’iyyar da ke Wuse 2 ta ke shirya irin wannan taron. Sai a wannan lokacin ne aka yi taron a Fadar Shugaban Kasa.

Shugaba marigayi ‘Yar’Aduwa ya taba shirya taron masu ruwa da tsakin PDP a ‘Yar’Adua Centre, Abuja.

Ba a dai san dalilin shirya taron a Zauren Majalisar Fadar Shugaban Kasa ba.

Sai dai kuma idan za a iya tunawa, kafin shirya taron, ‘yan sanda sun kewaye hedikwatar APC, sakamakon rikicin da ya rirnike jam’iyyar.

Share.

game da Author