Gwamnatin jihar Kaduna, karkashin ma’aikatar kiwon lafiya, wadda Amina Baloni ke shugabanta ta sahida cewa daga watan Afrilu, gwamnatin Kaduna za ta rika biyan ma’aikatan lafiya dake aikin kula da masu dauke da Coronavirus alawus duk rana.
Kwamishina Baloni ta ce za rika biyan su ne saboda sadaukar da kansu da suka yi wajen kula da wadanda suka kamu da cutra a jihar.
Sanarwar tace za a rika biyan ma’aikatan lafiya dake kula da masu fama da coronavirus naira 5000 duka rana. Sannan Kuma wasu 10,000, manyan su kuma 15,000.
Ta ce hakan zai kara musu kwarin guiwa wajen kula da marasa lafiya da kuma kiyaye kansu a wajen duba marasa lafiya. Baya ga tsarin inshorar da gwamnati ta saka su ciki.
Baya ga haka kuma suma ma’aikatan lafiya a asibitocin jihar da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na jihar duk an kara musu kashi 10% na albashin su duk wata.
Shima gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi tattaki ta musamman ya ziyarci likitocin da suka duba shi a lokacin da bashi da lafiya domin yi musu godiya bisa kulan da suka bashi.