Dan majalisar Kaduna dake wakiltar Zariya a Majalisar Dokokin jihar Suleiman Dabo ya aika wa shugaban majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamilla wasika ta musamman game da hauhawar farashin kayan abinci da na masarufi a Kasar nan.
Honarabul Dabo ya ce bisa ga binciken da yayi a jihar Kaduna, hauhawar farashin kayan abinci da na masarufi da ake samu ba daga rashin hada-hadar mutane bane, ‘Yan kasuwa ne ke gaban kansu suna tsawwala wa mutane tsada don cin kazamin riba.
” Wannan abu ya na neman a gaggauta duba shi tun da wuri kafin yakai musamman talaka ya baro. Tsadar kayan abincin yayi yawa matuka.
” Ina kira ga shugaban majalisar tarayya, da ya tilasta majalisar ta duba wannan kuka da ya mika gaban ta domin ba wai a Kaduna inda ya ke zaune ba, tsadar abincin ya karade ko-ina-ne a fadin kasar nan. Mutane na kuka matuka.
Ita dai wannan shimfidaddiyar wasika da Honorabul Dabo ya aika wa shugaban majalisa ya zo akan gaba ne domin kuwa mafi yawan mutanen kasar nan na fama da matsanancin tsadar abinci.
A daidai mutane na killace a gidajen su saboda bin dokar gwamnati na dakile yaduwar cutar coronavirus, yan kasuwa kuma suna sheke ayar su a kasuwanni. Ko ka siya ko ka bari. Sun tsawwala wa kayan abinci da masarufi kudi ta yadda mutane da dama basu iya siya.
A karshe Honarabul Dabo ya roki kakaki Gbajabiamilla da majalisar kasa ta duba wannan al’amari cikin gaggawa.