‘Yan tireda na kukan karancin tumatir a Kano, yayin da kwari suka sake dirar wa gonakin tumatir

0

Farashin danyen tumatir ya kara tashi sama a Arewacin Najeriya, sakamakon sake mamayar gonakin tumatir da wani kwaro mai suna Tuta Absoluta ya yi.

PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda wadannan kwari suka lalata gonakin tumatir masu dimbin yawa a Kano.

Shugaban Masu Noman Tumatir na Najeriya (TOGAN), Abdullahi Ringim, ya ce kwarin Tuta Absoluta sun bulla a jihohin Kaduna da Katsina, suna lalata gonakin da ake noma tumatir a cikin Afrilu.

Cikin 2016 cutar Tuta Absoluta ta barke, wacce ta lalata kusan kashi 80 bisa 100 na tumatir. Hakan ya haifar da dimbin asarar tumatir, hauhawar farashin sa da sauran kayan miya a Kasuwa.

Baya ga tunatir, an ce kwarin har yalo da dankali duk ba su bari ba.

Cikin shekarar 2006 cutar ta bulla a Spain, daga nan kuma ta ci gaba da bulla sauran kasashe.

Kafin dirar ta Najeriya, cutar tumatir din ta fara yin mummunar illa a Nijar da Senegal.

Cikin 2015 ta fara bulla a Daura, sai Kano da kuma Ogun cikin shekarar. Daga nan kuma ta fantsama a sauran jihohin kasar nan.

An ruwaito cewa bullar wadannan kwarin ne ya janyo rufe masana’antar sarrafa tumatir ta Dangote da ke Kano, cikin 2015.

Cikin 2016 sai da ta kai gwamnatin jihar Kaduna ta da dokar-ta-bacin yaki da kwarin Tuta Absoluta a gonakin tumatir din jihar.

‘Wannan cutar tumatir za ta kara kawo karancin tumatir a kasar nan, kuma manoman da suka ramci kudi a tsatin ‘Anchor Borrowers, zai yi wuya su iya biyan kudaden da suka karba.” Inji Abdullahi Ringim.

“Sannan kuma fatashi zai karu, saboda karancin samun tumatir din ya wadaci ko’ina, zai sa farashin sa hauhawa.” Inji shi.

“Gwamnatin Tarayya ta hannun Ma’aikatar Gona, ta yi kokarin samar da maganin kashe cutar. Amma an samu matsala. Saboda duk shekara.”

Sai dai kuma a yanzu ya ce tun da cutar ta dawo, gwamnati ba ta yi wani hobbasa ba a cikin 2020 din da ake ciki.

“Tsayawa jinkirin dogon-Turanci da gwamnati ke yi, kafin ta dauki mataki, babbar matsala ce. Kafin a yi wani abu nan da wata uku, lokacin tumatir har ma ya wuce.”

Micheal Kanu na Ma’aikatar Noma, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa cutar Tuta Absoluta mai lalata kwari, ta samu gindin zama a kasar nan.

Sai dai kuma ya yi bayanin matakan da gwamnati ta rika dauka wajen dakile cutar.

Share.

game da Author