El-Rufai ya kara makonni biyu na zaman Kulle a Kaduna, an kara kwana daya na walwala

0

Gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya kara saka makonni biyu na zaman kulle a jihar Kaduna sannan kuma ya kara kwana daya na walwala.

A sanarwar da mataimakiyar gwamnan jihar tayi ranar Talata, Hadiza Balarabe ta ce daga ranar Litini mai zuwa za a rika samun damar yin walwala a ranakun Talata, Laraba da Alhamis, sannan kuma masu saida abinci za su rika fitowa, fokanaza, masu ‘yan gyare-gyare, makanikai, masu Walda da ababen da ba a rasa za su rika fitowa suna sana’a.

Wannan dama bai hada da masallatai, Coci-coci, Kasuwanni, gidajen kwallo, gidajen shakatawa da makarantu ba.

Gwamna El-Rufai ya ce zai zauna da shugabannin addinai, shugabannin kasuwanni, masu makarantu domin tsara yadda za a dawo aiki sannu a hankali.

Su kuma ma’aikatu za su yi amfani da wannan makonni biyu da aka kara na Kulle domin tsara yadda ma’aikatan su za su rika aiki idan suka dawo aiki ta hanyar wawware wajen zama da saura su a ofisoshin su.

Share.

game da Author