Gwamnatin Najeriya da mutanen kasar musamman mazauna garin Legas sun kasa kunne da zura idanu domin ganin ranar da za a kaddamar da matatar mai mallakin attajiri, Aliko Dangote da yake ginawa a garin Legas.
Ana sa ran za a kammala aikin gina wannan matata tuna shekarar da ta gabata, wato 2019.
A wani bincike mai zurfi da bin diddigi da PREMIUM TIMES ta yi ta bankado yadda mahukuntan wannan kamfani suka yi kunnen uwar-shegu da dokokin dakile yada cutar CORONAVIRUS da aka saka a kamfanin ta hanyar tilasta wa ma’aikata dole su yi aiki ba tare da an sanar musu su da kayan samun kariya daga kamuwa da kwayoyin cutar ba.
Sannan duk da sanin yadda aka ci gaba da ayyuka a wannan katafaren kamfani gada-gadan a lokacin da aka saka dokar hana walwala, rundunar ‘yan sanda sun toshe kunnuwar kuma sun nuna cewa basu san hakan na faruwa ba.
A dalilin haka kuwa a ranar 27 ga Afrilu mazauna unguwannin Eleko, Tiye, Idasho, Akodo da Lekki dake makwabtaka da wannan kamfani suka gudabar da zanga-zangar adawa da yadda ake dawainiya da ma’aikatan wannan matata, tare da yin jigilar manajojin su daga kwatas dinsu ana ratsawa ta wadannan unguwanni tare da ‘yan sanda suna kula da tsare su amma mazaunan idan suka nemi watayawa ko da ko ta ‘yar lalura ce sai Jami’an tsaro su diran musu.
” Hatta manya-manyan motocin aikin su zaka ga suna zirga-zirga daga kwatas din zuwa wurin aiki tare da ‘yan sanda na gadin su amma mu mazauna unguwannin kusa da wannan matata ana muzanta mana, wai an hana fita ko walwala na ‘Lokdan’.
Wani ba-Indiye mai suna Satyendra Sharma, wadda shi jami’in kiwon Lafiya ne dake aiki a bangaren masana’antar sarrafa taki ne ya fara kamuwa da Korona a wannan kamfani cikin ma’aikata.
Sai dai kuma ba a bayyana rasuwar wannan ma’aikaci ba, an yi ta rufa-rufa da hakan domin ba a so a sani.
Bincike ya nuna cewa an kwantar da Satyendra Sharma a wani asibiti mai zaman kansa da ke rukunin gidaje na Saphire, mai suna Jajo.
Wani abokin aikin Sharma da ya bukaci a sakaye sunan sa ya shaida wa wakilin mu yadda Sharma yayi ta fama da rashin lafiya na tsawon kwanaki da ya kai ga wani likitan asibitin ya umarci da a garzaya da shi hedikwatar asibitin.
” Wannan likita ya koka kan yadda rashin lafiyar da Sharma ke fama da shi ke dada faskara sannan kuma ma’aikatan asibiti dake duba shi basu kula da kiyay kansu, wato basu saka kayan Kare jikin su ba.
Haka dai aka yi dawainiya da Sharma, har ya kai ga Jami’an hukumar NCDC suka yi masa gwajin Korona kuma suka tabbatar ita ce yayi ta fama da har ya rasu.
Bayan shi dukka wadanda aka yi wa gwaji cikin abokanan aikin sa da yayi mua’mula da su duk ya nuna suna dauke da kwayoyin cutar.
A dalilin haka ne kuma wani da ga cikin Injiniyoyin wannan kamfani, kuma ba Indiye mai suna Shivajeet Kumar ya rataye kan sa a watan Afrilu.
Majiya ta ce Kumar ya kashe kan sa ne bayan an bayyana masa cewa shima ya kamu da cutar, kuma yana da bayanin cewa ‘yan uwan a kasar Indiya suma na fama da wannan annoba.
Sai dai wannan Jarida bata tabbatar da haka kai tsaye ba.
Ma’aikatan wannan kamfani sun gudabar da zanga-zangar nuna rashin jin dadin su kan yadda mahukuntar kamfanin ke tilasta musu su yin aiki dole sannan kuma ba a biyan su albashi.
Daga baya dai gwamnatin jihar Legas ta rufe wannan asibiti da aka kwantar da Sharma.
Wani maigadin asibitin ya ce sai da aka yi wa ma’aikatan asibitin duka gwajin cutar har shi.