Sufeto Janar, Gwamnatin Kano sun bi umarnin kotu, sun cire kwadin da suka garkame Kamfanin Tiamin

0

Gwamnatin Kano da Sufeto Janar din ‘Yan sandan Najeriya sun bi umarnin kotu, da ta ce su bude Kamfanin shinkafa ta Taimin da suka garkame a Kano.

Idan ba a manta ba, gwamnatin Kano ta garkame Kamfanin shinkafa, Tiamin dake Kano a dalilin wai ta yi kusa da wurin da ake killace masu fama da Korona a jihar.

Tun a wancan lokaci mahukuntan kamfani suka musanta haka Inda suka ce tsakanin Kamfanin da inda gwamnati ta killace masu fama da Korona sai an yi tafiyar akalla kilomita sama da 20 kafin a akai.

A bisa wannan dalili ne Kamfanin ta ce idan dai ba bita da kulli ake mata ba babu wani dalilin dakatar ta aikin ta.

Daga nan sai ta garzaya kotu.

A zaman da kuto ta yi bayan sauraren korafin Tiamin da ana gwamnatin Kano, kuma bayan ta gudabar da nata binciken sai ta yanke hukuncin cewa maza-maza Gwamnati ta rabu da wannan kamfani, ta bude ta, cewa bata aikata laifin komai ba.

Sannan kuma ta umarci Gwamnati ta biya Kamfanin naira 300,000 na bata mata lokaci da tayi.

Daga baya gwamnati bata amince da hukuncin kotun ba sai ta daukaka.

Amma kuma kwatsam sai aka wayi gari da kanta ta kwashe kayanta, ta kwance kaca-kacar da ta sarkake kofofin Kamfanin da kwadin ta tara gaba.

Kamfanin sarrafa shinkafa ta Tiamin na sarrafa shinkafa akalla tan 320 a duka rana kuma tana da ma’aikata sama da 220, da kuma ma’aikatan wucin gadi 100.

Share.

game da Author